Dakarun sojojin Najeriya sun halaka ‘yan ta’addan Boko Haram da dama a wani bata kashi da suka yi a yankin Banki na karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa sojojin wadanda suka fito daga bataliya ta 151 tare da hadin guiwar ‘yan sakai (CJTF) sun afkawa maboyar ‘yan ta’addan a kauyen Gauri a ranar 30 ga watan Oktoba.
‘Yan ta’addan Boko Haram sun kwashi kashin su a hannu a wajen sojoji
‘Yan ta’addan kuma suna amfani da maboyar ta su wajen ajiyar shanun satar da suka kwato.
“Fiye da mutum goma sha biyar aka halaka nan take,” A cewar wata wani soja wanda aka fafata yakin da shi.
“Dole ta sa ‘yan ta’addan suka arce suka bar shanun da suka sace bayan da yawa daga cikin su, suka samu munanan raunika.”
Majiyar ta kuma bayyana cewa sojojin sun halaka wasu daga cikin ‘yan ta’addan da suka arce suka kira karin mayaka.
Sai dai, sojoji biyu sun rasa rayukan su a yayin bata kashin.
‘Yan ta’addan sun karo mayaka akan babura, amma sojojin sun fatattake su bayan an yi bata kashi.” A cewar majiyar
“Mun halaka karin mutum bakwai daga cikin su a fadan da ya sake barkewa, amma abin takaici biyu daga cikin jajirtattun sojojin mu sun kwanta dama yayin da wasu biyar kuma suka samu raunika yayin da suka bi bayan ‘yan ta’addan da suka arce.”
Ba a samu jin ta bakin kakakin hukumar sojojin kasa Onyema Nwachukwu, game da lamarin ba.
ISWAP ta halaka ‘yan ta’addan Boko Haram da dama a wani sabon karon batta
A wani labarin na daban kuma, mayakan ISWAP sun halaka ‘yan ta’addan Boko Haram da dama a jihar Borno.
Kungiyar ‘yan ta’addan ISWAP ta halaka mayakan Boko Haram mutum takwas a jihar Borno a fada da ya barke a tsakanin su.
A cewar Zagazola Makama, wata jarida wacce ta mayar da hankali kan abubuwan dake aukuwa a yankin tafkin Chadi, kungiyoyin ‘yan ta’addan biyu sun fafata ne a ranar Alhamis a yankin Krinowa na Marte
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana raayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com