Wani matashin ango mai suna Shehu Lili Kofar Atiku ya rigamu gidan gaskiya sa’o’i ashirin da hudu bayan an daura maaa aure a jihar Sokoto.
Wani abokin angon, mai suna Shamsudeen Buratai shine ya tabbatar da aukuwar lamarin. Shafin LIB ya rahoto.
Buratai ya bayyana cewa Shehu Lili ya rasu bayan yayi fama da ‘yar gajeruwar rashin lafiya.
Angon ya rasu sa’o’i kadan bayan an daura masa aure
A cewar Buratai, an daura auren angon ne a ranar Lahadi 5 ga watan Oktoba 2022, da misalin karfe biyar na yamma a unguwar Kofar Atiku sannan ya rasu da safiyar ranar Litinin.
“Shehu abokina ne tun na yarinta kuma dan’uwa na tsawon fiye da shekara 30. Yana fama da matsananciyar malaria wacce take taso masa duk lokacin sanyi. Kamar kowace shekara, ciwon nasa ya taso masa a bana a cikin watan Disamba, inda ya sha magunguna ya samu lafiya.” A cewar sa.
“Da safiyar yau misalin karfe tara na safe, ya fito inda muka gaisa yadda muka saba. Kwatsam kawai sai ya fara jin wani bakon yanayi inda yace manan yana tunanin ciwon malaria ne yake kokarin dawo masa. Kafin mu yi aune kawai har ya fadi kasa, shikenan karshen sa kenan.” Inji Shamsu.
Tuni dai har an binne mamacin bisa yadda shari’ar musulunci ta tanada.
Muna addu’ar Allah (SWT) ya jikansa da rahama ya gafarta masa, yasa aljannah ta zama makomana gare sa, mu kuma idan tamu ta zo yasa mu yi kyakkyawan karshe na cikawa da Imani. Ameen summa Ameen.
Budurwa ta fasa auran angonta ana saura kwana uku daurin aure, ta bayyana dalilan ta
A Wani labarin na daban kuma, wata budurwa tace ta fasa auran angon ta ana gab da a daura musu aure.
Wata budurwa ta fasa auran mijin da zata aura ana saura kwana uku a daura musu aure.
Wata shahararriyar mai watsa labarai, Amanda Chisom, itace ta sanya hoton wallafar da budurwar tayi na cewa ta fasa auran.
A cikin rubutun da budurwar tayi a shafin Twitter, tace koda yaushe mijin da zata aura yana ce mata kudin sa na a asusun da ba a tabawa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com