Wata mata ta yi murnar Kammala jami’a tare da iyayenta da ‘yan uwanta kamar yadda ta bayyana wa duniya, Legit.ng ta ruwaito.
A bidiyon an ga inda ta tafi da gudu ta shiga shagon siyar da ruwan leda inda mahaifinta ke sana’arsa ta rungume shi.
Mahaifin nata cike da farinciki ya durkusa da guiwoyi kasa yayin da yake godiya ga Ubangiji akan ni’imar da yayi masa ta kammala karatu da diyarsa tayi.
A bidiyon wanda ya bazu a kafar TikTok, bayan yayanta ya sanya mata hannu ne tayi gudu zuwa shagon mahaifinta.
An ga inda mahaifin nata ke wakoki na murna har ya kai ga durkusawa kasa don yi wa Ubangiji godiya.
A bidiyon, yarinyar ta bayyana cewa da sana’ar fiyo wota iyayenta su ka dauki nauyin karatunta har ta gama.
An ga inda mahaifiyarta ke murna inda aka ga wata yarinya tana siyar wa kwastomomi ruwan, ta yuwu kanwarta ce.
2023: Sai ubangiji ya hukunta mu idan bamu goyi bayan Tinubu ba -CAN reshen jihar Legas
Shugabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Legas, sun bayyana goyon bayan su ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kungiyar na jihar Reverend Stephen Adegbite, shine ya bayyana hakan a ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Za su fuskanci fushin ubangiji idan ba su goyi bayan dan takarar ba
Adegbite yace ubangiji zai hukunta kungiyar addinin idan ta kasa goyon bayan Tinubu a zaben 2023.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com