Da alamu wannan fitaccen ɗan daudun da ya shahara a kafafen sada zumuntar zamani mai suna James Brown ya dakata da harkar daudu, Legit.ng ta ruwaito.
Yayin da yake son tabbatar wa masoyansa a kafafen sada zumunta, ya kira kansa da saurayin da ake yayi inda yace yanzu matar aure yake nema.
Jama’a da dama sun yi ta cece-kuce yayin da wasu ke ganin kamar ba dagaske yake ba, wasu kuma su na ganin gaskiyarsa kenan saboda ya sauya rayuwa.
Ya dakata da shiga mata a hotunan da yake wallafawa na kwanannan inda ya koma siffarsa ta asali wato namiji.
A baya kowa ya san yadda yake sanya sutturu irin na mata, yayi kitso sannan ya sanya kumbuna tamkar mace kuma ya kira kansa da sarauniyar nahiyar Afirka.
A wannan datsin kuwa, har kiran kansa da saurayi yayi, inda yace yanzu shi ake yayi kuma yace yana neman matar aure.
Ya wallafa hakan ne a shafinsa sanye da tufafi irin na maza inda yace:
“Saurayin da ake yayi a gari, ban da aure kuma ina neman matar da zan kira matata.”
Matar aure ta shiga dimuwa bayan ta samu juna biyu da direbanta, bidiyon ta ya dauki hankula
Wata matar aure ‘yar kasar Ghana ta bayyana yadda ta ci amanar mijinta da direbanta wanda yanzu shine uban ‘ya’yanta.
Bayan ta kasa samun sukuni bisa abinda ta aikata, matar auren ta tonawa kan ta asiri inda ta bayyana yadda ta samu juna biyu sau biyu tare da direbanta.
Da take bayyana abinda ya faru, matar auren wacce aka sakaya sunan ta, tace aurenta da mijinta ya kai shekara shida, amma bata samu juna biyu ba. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Ta yanke shawarar zuwa ganin likita wanda yayi mata gwaje-gwaje inda ya gaya mata cewa babu wata matsala a tattare da ita.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com