36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Yadda aka gano wata karamar yarinya a raye cikin rijiya kwana uku bayan ta bace

LabaraiYadda aka gano wata karamar yarinya a raye cikin rijiya kwana uku bayan ta bace

An tsinci wata karamar yarinya Lydia Azatyom, mai shekara uku a duniya a cikin wata tsohuwar rijiya, kwanaki uku bayan tayi batan dabo a unguwar Tudun Wada ta Jos, babban birnin jihar Filato.

Ganin karshe da aka yiwa karamar yarinya ya auku ne a ranar Alhamis 27 ga watan Oktoba, tana wasa da kawayenta a kofar gidan su kafin bacewar ta.

Duk wani kokarin iyayenta da makwabta na ganin an gano inda take yaci tura, har sai zuwa bayan kwana uku, lokacin da wani Dauda Dung ya tabbatar da cewa an gano ta.

Wani matashi ya gano yarinyar a cikin rijiyar

Shafin LIB ya ambato cewa wani matashi ne ya gano yarinyar a cikin wata tsohuwar rijiya a wani kango dake unguwar.

An tattaro cewa matashin yaje kangon ne domin yin bayan gida inda yaji karar alamun motsi a cikin rijiyar wacce bata da ruwa.

Ginin kangon dai an dade ba a amfani da shi inda yanzu aka mayar da shi wurin zubar da shara da yin bahaya.

Ba a da tabbacin fadawa tayi ko kuma wani ne ya jefata cikin rijiyar

Lydia ta samu raunika a wajen kanta inda aka garzaya da ita asibiti inda take cigaba da samun kulawar da ta dace.

Har yanzu dai ba a da masaniyar cewa ko yarinyar bisa tsautsayi ta fada cikin rijiyar ba ko kuma wani ne ya jefata ciki.

Yarinya ta sha kuka bayan mamarta ta shiga gasar rawa don samun injin niƙa ta faɗi

A wani labarin na daban kuma, wata yarinya ta sha kuka bayan mamarta bata samu nasara ba a gasar rawan da ta shiga.

Wata ‘yar Najeriya ta dauki hankalin mutane da dama bayan an ganta a bidiyo tana rusa kuka saboda mahaifiyarta ta shiga gasar rawa don samun injin nika amma ta fadi, Legit.ng ta ruwaito.

Wata ma’abociya amfani da kafar TikTok mai suna @amazing_people111, ta wallafa wani bidiyo inda ta bayyana cewa mata goma sun shiga wata gasar rawa don su samu injin nika.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe