Akalla fasinjoji mutum 11 ne suka kone a wani mummunan hadarin mota da ya auku a jihar Enugu.
Lamarin ya auku ne a daren ranar Lahadi a yankin 4-corner na kan hanyar babban titin Enugu-Port Harcourt.
Fasinjojin na kan hanyar zuwa jihar Kano
Fasinjojin sun taso ne daga jihar Imo inda suke kan hanyar su ta zuwa jihar Kano. Jaridar The Cable ta rahoto.
A wata sanarwa da kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ya fitar a ranar Litinin, yace akwai fasinjoji sha daya a cikin motar lokacin da ta kama da wuta
“Motar ta aukawa wata babbar mota ne dake tsaye a Akegbe-Ugwu, akan babban titin Enugu-Port Harcourt inda ta kama da wuta wacce tayi sanadiyyar konewar mutum 11 daga cikin fasinjojin kafin a kawo musu agajin gaggawa.” A cewar sanarwar.
“An kai su zuwa asibiti inda likitocin dake a bakin aiki suka tabbatar da sun rasu.”
‘Yan sanda sun fara gudanar da bincike kan lamarin
Kakakin hukumar ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa bangaren zirgar-zirgar ababen hawa na hukumar ya fara gudanar da bincike domin gano ainihin abinda ya haddasa aukuwar hadarin.
A halin da ake ciki, wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba, sun ce fasinjoji 14 ne suka rasu a hadarin, yayin da mutum daya ake duba lafiyar sa asibiti.
Yar TikTok ta sha caccaka bayan wallafa bidiyonta tana rusa kuka bayan tafka hadari
A wani labarin na daban kuma wata mai amfani da TikTok ta sha caccaka bayan ta wallafa bidiyonta tana sharbar kuka bayan tayi Hadari.
Jama’a sun yi caa akan wata budurwa wacce babu dadewa da tafka mummunan hadari a ranar 10 ga watan Augusta, ta dauki kanta bidiyo inda ta wallafa a TikTok, LIB ta ruwaito.
Mutane da dama sun tausaya mata yayin da wasu su ka dinga caccakarta su na ganin cewa bata cancanci tausayawa ba tunda har ta iya tura bidiyon da ta dauka da kanta a TikTok.
A hadarin da ta yi an ga yadda jini ya dinga kwarara daga kanta kasancewar ta ji mummunan rauni.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com