27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Dan Najeriya yayi wuff da wata kyakkyawar baturiya, bidiyon yadda take masa hidima ya dauki hankula

LabaraiDan Najeriya yayi wuff da wata kyakkyawar baturiya, bidiyon yadda take masa hidima ya dauki hankula

Wani matashi dan Najeriya mai amfani da @kanorsamuel223 a manjajar TikTok ya saka wani bidiyon budurwar sa Baturiya a kafar.

Wani bangare na daga cikin bidiyon ya nuna kyakkyawar baturiyar na amfani da tukunyar gas tana soya masa filanten. Ta nuna cewa lallai ita fa taga wurin zama.

Matashin ya samu kyakkyawar baturiya

Idan da ba domin yanayin kalar fatar jikinta ba, da sai ayi tunanin cewa ‘yar Najeriya ce bisa yadda take gudanar da dafa abincin.

Mutane da dama sun yi tururuwa zuwa bangaren yin sharhi domin tambayar matashin yadda akayi ya samu wannan kyakkyawar baturiyar a matsayin budurwar sa.

Ku kalla bidiyon a nan.

Bidiyon ya dauki hankula sosai

Akwai akalla sama da mutum 400 da suka yi sharhi a kan bidiyon, yayin da sama da mutum dubu sha bakwai suka danna alamar so akan bidiyon.

Alex George ya rubuta:

“Pablo kayi kokari, lokacin ka ne na tunawa cewa lallai akwai so na gaskiya, ‘yan’uwanta kar mu yasa nace maka nagode.”

halo ya rubuta:

“Dan’uwa ya samu nasara a rayuwa!!! yooooooooo!”

Dandy McCarthy ya ributa:

“Surkullenka mai karfi ne.”

Tik Toker ya rubuta:

“Ya samu katin zama dan kasa.”

washy ya rubuta:

“Har yanzu ina ta tunanin abinda za a samar.”

So makaho ne: Zukekiyar Baturiya mai arziki ta iso har Najeriya inda tayi wuff da gurgu

A wani labarin na daban kuma, wata Zukekiyar Baturiya mai arziki tayi wuff da wani gurgu a Najeriya.

Bayan sun yi auren kotu a 2015, wata baturiya mai suna Ranti Jacobs Agbaminoja ta zo har Najeriya don auren saurayinta, Omotayo Agbaminoja wanda gurgu ne inda aka yi shagalin a 2022, Legit.ng ta ruwaito.

Baturiyar wacce ke da tushen Yarabawan Najeriya ta sanar da BBC News Yoruba a tattaunawar da su ka yi da ita cewa sun hadu da Omotayo ne a wata coci da ke Maryland.

Daga fara abota da juna, sai su ka fara soyayya wacce duk da hakan bata taba tambayarsa yadda aka yi ya fara amfani da keken guragu ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana raayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe