Wata budurwa ta fasa auran mijin da zata aura ana saura kwana uku a daura musu aure.
Wata shahararriyar mai watsa labarai, Amanda Chisom, itace ta sanya hoton wallafar da budurwar tayi na cewa ta fasa auran.
A cikin rubutun da budurwar tayi a shafin Twitter, tace koda yaushe mijin da zata aura yana ce mata kudin sa na a asusun da ba a tabawa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Budurwar ta fasa auran
Duk da rokon da budurwar ta sha yi, saurayin yace zai biyata duk abinda ta kashe a bikin. Daga karshe dai ta fasa auran bayan ta samu shawara daga wajen wani masani kan lamuran aure.
A kalamanta:
“Wannan mutumin bai bayar da ko asi ba kuma daurin auren saura kwana uku, yana ta cewa kudin sa na asusun da ba a tabawa, sannan zai biya ni daga baya.”
Ba ya da ko sisi
Da take magana akan hukuncin da budurwar ta yanke, Amanda Chisom tace:
“Mutumin da ba ya da ko asi, na sawa a baki kawai yake samu, ba ya da mota, ba gida mai kyau amma kudin sa na asusun da ba a tabawa. Ya nuna tsantsar wauta wacce za a iya yin gadon ta.”
Mutane sun tofa albarkacin bakin su
Vivian Nwuzor ta rubuta:
“Eh kin yi abinda ya dace, yaje can ya karata da asusun da ba a tabawa.”
Adeshola Mercy Dada ta rubuta:
“Eh kin yi daidai. Wannan wanda zaki auran dan 419 ne.”
Nkuku-Ogechi Joy Victor ta rubuta:
“Kin auna arziki ‘yar’uwa, da haka ake farawa. Kafin ki ankara har kin fara biyan na cefane. Mutuminki ba ya da ko sisi.”
Matar aure ta shiga dimuwa bayan ta samu juna biyu da direbanta, bidiyon ta ya dauki hankula
A wani labarin na daban kuma, wata matar aure ta ci amanar mijinta da direbanta, har yayi mata ciki.
Wata matar aure yar kasar Ghana ta bayyana yadda ta ci amanar mijinta da direbanta wanda yanzu shine uban yayanta.
Bayan ta kasa samun sukuni bisa abinda ta aikata, matar auren ta tonawa kan ta asiri inda ta bayyana yadda ta samu juna biyu sau biyu tare da direbanta.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana raayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com