Shahararriyar mai amfani da kafar sada zumunta ta facebook Jamila Ibrahim ta bayyana cewa ba daidai bane amare su riƙa yin kishi ko gasa da uwargida a gidajen mazajen su ba domin kuwa ita tasha wahalar mijin.
Jamila wacce ita ce keda dandalin Facebook na home of Solace ta bayyana haka ne a wani rubutu data wallafa a shafinta da safiyar Lahadin nan.
Tace tana mamakin yadda wasu amaren ke yi na yanda suke ƙoƙarin nuna kishi da gasa da uwargida wacce su zuwa suka yi suka tarar da ita da mijin, ba tare da sun san irin faɗi tashin da ta sha tare da shi ba.
Bai kamata ace duk abinda akama uwargida sai an miki ba
Ta ƙara da cewar bai kamata amarya ta riƙa cewa duk abinda miji yayi ma uwargida wai itama dole san an yi mata ba.
“Ina mamakin wasu amare da suka je suka sami uwargida da mijinta da sukayi aure tun baida komai sannan su dinga kishi da ita dan miji yafi kashe mata kudi.
“Wasu ma harda cewa duk abunda za’awa uwargida sai dai ayi masu iri daya. Naga wacce ma tazo ta sami uwargida da jeep tace lallai sai dai miji ya siya mata irin na uwargidan.
“Malama ke da kika zo jiya jiya har zakiyi graduating daga nursery ki shiga university , a Ina aka taba hakan?” inji Jamila Ibrahim.
Komai a hankali ake bin shi
Jamila ta janyo hankulan mata musamman ma dai amare da kuma waɗanda ke shirin auren mijin da yake da wata matar kafin su akan su sani cewa komai sannu a hankali ake bin shi ba tare da yin gaggawa ba tunda basu san irin gwagwarmayar da aka sha kafin ta zo ba.
Ta ƙara da cewar kada amarya ta ɗauka wai ko don miji baya son uwargida ne ko kuma wai don ya gaji da uwargidan ne ya aurota, tace ba haka bane, iyaka dai mijin yana ƙoƙarin cika umarnin Ubangiji ne.
“Komai gradual process ne , ba’a komai da gaggawa , abunda Kai bakaso ayi Maka Kar kayiwa wani , bakisan irin gwagwarmaya da sukayi tare ba , bakisan wani irin rayuwa sukayi ba ke kinzo kin samesu kina son kiyi gasa da ita.
An auro uwargida don cika umarnin Ubangiji ne
“Ba wai baya sonta ne ya auro ki ba , ba wai ya gaji da ita bane ya auro ki , ya auro ki ne Dan cika umarnin Allah da manzon sa.
Daga ƙarshe dai ta ja hankalin amaren akan su kasance masu haƙuri da biyayya ga mazajen su ba wai ya zamto suna gasa ko rigima da uwargida ba.
“Don haka kowacce amarya ta natsu ta kama kanta har layi ya biyo ta kanta , iya biyayyar ki iya kulawa da zaki samu cikin kwanciyar hankali, ba wai gasa da rigimar zaisa ayi maki abunda kikeso ba.”
A wani labarin na daban kuma, wata jaruma tace babban kuskure ne barin iyaye su zaba muku wanda zaku aura.
Wata tauraruwar jarumar wasan kwaikwayo ta bayyana ra’ayin ta kan zaɓar miji da wasu daga cikin iyaye suke ma ‘ya ‘yansu a yayin da suka kai munzalin aure.
Jarumar mai suna Eriata Ese ta wallafa rubutun a shafin ta na Snapchat inda ta bayyana cewa barin iyaye su zaɓa ma ki/ka miji ko mata shine babban kuskuren da mutum zai iya yi a rayuwar shi.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com