34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Babban kuskure ne barin iyaye su zaba muku wanda zaku aura – Jarumar Fim

LabaraiBabban kuskure ne barin iyaye su zaba muku wanda zaku aura - Jarumar Fim

Wata tauraruwar jarumar wasan kwaikwayo ta bayyana ra’ayin ta kan zaɓar miji da wasu daga cikin iyaye suke ma ‘ya ‘yansu a yayin da suka kai munzalin aure.

Ta wallafa batun a shafinta na sadarwa

Jarumar mai suna Eriata Ese ta wallafa rubutun a shafin ta na Snapchat inda ta bayyana cewa barin iyaye su zaɓa ma ki/ka  miji ko mata shine babban kuskuren da mutum zai iya yi a rayuwar shi.

Ta ƙara da cewar yadda iyaye ke yin abubuwa akan ganin cewa daidai suke yi musamman domin taƙamar cewa su sun daɗe yana janyo daƙilewar rayuwar ‘ya ‘yan nasu.

Son kai ne iyaye suke yi

Tana ganin cewa abun kamar son kai ne da iyaye suke yi ba tare da sun tsaya sun duba wane irin ra’ayi ne yaran nasu suke da shi ba.

Tace a mafi yawan lokuta iyaye kawai na zaɓar wa mutum abokin rayuwa ne kawai don ganin cewa zai amfani zuri’arsu.

Ta kuma ƙara da bayyana cewa da na sani ka iya biyo wa baya idan mace ta auri miji ko kuma miji ya auri matar da halinsu bai zo daidai ba.

Iyaye na tursasa ‘ya ‘yansu auren wanda basu so

Jarumar ta kuma bayyana cewa lokuta da dama zaka ji wasu ma’auratan na ƙorafin kan yadda iyayen su suka tursasa su yin auren da basu da sha’awa a ransu, ma damar dai su ya yi musu daidai.

Haka nan kuma jarumar ta ƙara da cewar wani abu da yafi damunta shine yadda iyaye ke nacewa akan ƙabilanci wajen yin aure. Ta ce sai kaga wai iyaye sun nace sai ɗan ƙabilar su, ko kuma suce ba za’a auri ɗan ƙabila kaza ba da sauransu.

A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar labour party Peter Obi ya bayyana cewa idan Allah yasa ya ci zaɓe a kakar zaɓen 2023 mai zuwa to ba zasu tsaya suna tuhumar laifukan da gwamnatocin baya suka yi ba, zasu kafa gwamnatin matasa ba ta tsofaffi ba.

Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a garin Lafiya jihar Nasarawa a yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shi da yayi. Yace idan yaci zai maida hankali wajen magance matsalolin da suka addabi ƙasar ba tare da ya tsaya ɗora na wani laifi ba.

Ya shaida ma al’ummar jihar Nasarawa cewa zasu samu wadatattun hanyoyi, zasu samu ingantaccen shugabanci na shuwagabanni na gari ba waɗanda zasu riƙa ci da gumin su ba, The cable ta wallafa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe