Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun cafke dagacin Gidan Abba, Abubakar Ibrahim mai shekara 38 a duniya, a karamar hukumar Bodinga ta jihar Sokoto bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi.
An samu dagacin dauke da miyagun kwayoyi
Kakakin hukumar Femi Babafemi, shine ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja ranar Lahadi. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Babafemi yace an cafke dagacin ne dauke da kilogiram uku na tabar wiwi da kwayoyin exol-5 guda dubu hudu.
Jami’an hukumar sun cafke miyagun kwayoyi da dama
Dagacin yana daga cikin mutum 11 da jami’an hukumar NDLEA suka cafke a yayin kamen da suka yi a jihohi bakwai inda suka kwace kwayoyin opioids 991,320 da kilogiram 1,251kg na tabar wiwi da khat, da kuma kilogiram 46.637kg na methamphetamine, hodar iblis da tabar heroin.
A cewar sa, a tashar filin jirgin sama ta Murtala Muhammad dake Ikeje a Legas, jami’an hukumar NDLEA dake aiki a wurin shigo da kaya daga kasar waje na SAHCO a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba, sun cafke katon 15 dauke da kwayoyi 802,000 na Tramadol wadanda aka shigo da su daga Dubai na kasar hadaddiyar daular Larabawa (UAE) da birnin Karachi na kasar Pakistan.
“Yayin da katon 10 na Tramadol 225mg sun zo ne daga Dubai akan jirgin Ethiopian Airlines, katon hudu na Tramadol 225mg sun zo ne daga birnin Karachi na Pakistan akan jirgin Ethiopian Airlines.” Inji Babafemi.
Hukumar NDLEA ta cafke kwalaben Akuskura 26,000 a jihar Kano
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun kama wani fitaccen mai hada abinda aka sani da Akuskura a Kano.
Jami’an sun kama Qasim Ademola, inda suka same shi da kwalaben a kuskura har guda 26,600 wanda aka tanada domin rarabawa a fadin jihohin Arewa.
An kama kayan ne a ranar Alhamis 15 ga watan Satumba a kan hanyar Zaria zuwa Kano,akan Gadar Tamburawa, a jihar Kano .Wanda yake hadawa mai kimanin shekaru 39 wanda yakasance dan asalin jihar Oyo ne an kama shi ne ,tare da wasu mutum uku a wani samame da aka yi.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana raayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com