Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar labour party Peter Obi ya bayyana cewa idan Allah yasa ya ci zaɓe a kakar zaɓen 2023 mai zuwa to ba zasu tsaya suna tuhumar laifukan da gwamnatocin baya suka yi ba, zasu kafa gwamnatin matasa ba ta tsofaffi ba.
Peter Obi yace zai magance matsalolin da suka addabi ƙasar
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a garin Lafiya jihar Nasarawa a yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shi da yayi. Yace idan yaci zai maida hankali wajen magance matsalolin da suka addabi ƙasar ba tare da ya tsaya ɗora na wani laifi ba.
Ya shaida ma al’ummar jihar Nasarawa cewa zasu samu wadatattun hanyoyi, zasu samu ingantaccen shugabanci na shuwagabanni na gari ba waɗanda zasu riƙa ci da gumin su ba, The cable ta wallafa.
“Jihar Nasarawa zata samu cigaba sosai. Zaku samu hanyoyi nagartattu daga nan zuwa Abuja. Waɗannan irin abubuwan da zamu riƙa yi. Zaku samu ingantaccen shugabanci. Zaku ga jajurtattun mutane ba waɗanda zasu zo suna tattare muku dukiya ba.” inji Peter Obi.
Peter Obi ya buƙaci matasa su zaɓe su inda ya ƙara tabbatar ma da matasan na jihar Nasarawa cewa gwamnatin su zata fitar dasu daga talauci ta hanyar samar musu da hanyoyin dogaro da kai.
Zamu fitar da ku daga ƙangin talauci
“Zamu sanya kuɗi sosai domin mu tabbatar da cewa mun tsamin matasan jihar Nasarawa daga ƙangin talauci. Saboda haka ku goyi bayan mu.
“Kada ku zaɓi mutanen dake sace muku kuɗaɗe. Ba zamu satar muku kuɗaɗe ba. Muna nufin ku da alkhairi, muma matasa ne kamar ku ɗin nan.” inji shi.
Peter Obi ya ƙara zayyana cewa su ba zasu tsaya suna fakewa da cewar sun shigo ofis basu tarar da komai ba. Yace su matasa ne masu ilimi saboda haka zasu yi iya yinsu wajen ganin sun ciyar da ƙasa gaba.
“Mun shirya ma aikin namu. Ba zamu tsaya bada uzurirrika ba; ba zamu tsaya faɗa muku abinda mu tarar ba a sa’ilin da muka shiga ofis. Mu biyun nan matasa ne masu ilimi. Zamu iya tsayu kai da fata ba tare da wata damuwa ba. Zamu ciyar daku.” inji Peter Obi.
Gwamnatin mu ta mata da matasa ce bata tsofaffi ba
“Gwamnatin mu zata zamo gwamnati ce ta mata da matasa. Ba maganar gwamnatin tsofaffin mutane. Gidan gwamanti ba gidan ritaya bane, ba gidan tsofaffin mutane bane, zamu samar da jajirtacciyar gwamnati.
“Mun shirya ma aikin. Mun san matsalolin ku. Zamu samar da taki wadatacce ga manoma. Tsamu tallafi noma.” inji shi.
Peter Obi ya kuma ƙara da cewar gwamnatin sa zata fi mayar da hankali wajen ganin an bunƙasa harkar kamfanoni ta yanda za’a riƙa samar da abubuwan da ake buƙata a cikin ƙasa maimakon ace komai sai an shigo da shi.
“Zamu tsamo Najeriya daga halin cinyewa zuwa halin samarwa; ta hakan ne mutane da dama zasu samu ayyukan yi. Ko bamu goyon baya, kuje ku fara mana yaƙin neman zaɓe domin amfanin goben ku. Kada ku tsaya saurarar waɗannan mutane dake rarraba muku kudaɗe.” inji Peter Obi.
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda wani yaro ɗan shekara 15 ya kashe mahaifiyar shi kan hana shi shaye-shaye.
Wani yaro ɗan shekara 15 dake zaune a ƙauyen Osubeng, a gundumar Kwahu dake gabashin ƙasar Ghana ya kashe mahaifiyar shi sakamakon hana shi shaye-shaye da take yi.
Ance yaron mai suna Illiasu Amuni ya kashe mahaifiyar tashi mai suna Sakina Amuni ne dai ta hanyar buge ta da sanda sannan kuma ya yanka wuyan ta da wuƙa a yayin da take tsaka da aiki a gonar ta.
Wakilin majiyar mu ta Adom News wanda ya bibiyi labarin yadda abun ya samo asali ya bayyana cewa dama can baya yaron ya sha alwashin cewa lallai sai ya kashe mahaifiyar tashi saboda ta hana shi shaye-shayen tabar wiwi.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com