Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Kashim Shettima, ya bayyana lokacin da zai tuntubi dan takarar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Dr Rabiu Musa Kwankwaso.
Kashim Shettima yace zai tuntubi dan takarar ne a lokacin da ya dace kafin zuwan babban zaben shekarar 2023 dake kara matsowa. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Kashim Shettima, wanda yake bayar da lakca a wajen taron limaman birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a a matsayin daya daga cikin bakin da aka gayyata, yana ba’a ne ga tsohon dan majalisar tarayya, Garba Ibrahim Muhammad, wanda ya wakilci Sanata Kwankwaso a wurin taron.
Kashim Shettima na ganin kimar Kwankwaso
“Nayi alkawarin ba zan yi maganar cin mutunci akan sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba a gabadaya lokacin zabukan nan. Shugaba ne nagari sannan Insha Allah za mu zauna tare sannan mu fahimci juna a daidai lokacin da ya dace nan bada dadewa ba.”
“Wadanda suke shirin raba kasar nan ba za suyi nasara ba, sannan a saboda haka yakamata mu yi hakuri da junan mu sannan mu yi sadaukarwa,” A cewar Kashim Shettima.
Ko a bara an gudanar da irin wannan taron
Tunda farko a yayin jawabin sa, shugaban kwamitin ‘Committee of the FCT Imam Initiative (CFII)’, Imam Tajuddeen Bello, yace taron ya samu wakilcin limamai daga dukkanin jihohi 17 na Kudancin kasar nan wanda aka yiwa taken: “Limamai’ Hadin kai domin cigaban kasa.”
Yace an shirya irin wannan taron a shekarar da ta gabata domin limaman jihohi 19 na Arewacin kasar nan.
Yadda rigima ta barke tsakanin Kashim Shettima da Omoyele Sowore a wajen rattaba hannu kan zaman lafiya
An samu hargitsi tsakanin Kashim Shettima da Omoyele Sowore a wurin rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin ƴan takarar shugaban ƙasa na jamiyyu daban-daban da za su fafata a babban zaɓen 2023 dake tafe.
Taron wanda aka yi a ɗakin taron ƙasa da ƙasa (ICC) a Abuja ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, wanda kwamitin zaman lafiya na ƙasa ya shirya sannan ya samu halartar kusan dukkanin ƴan takara na jamiyyu face Asiwaju Bola Tinubu na jamiyyar APC.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana raayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com