Shugaban jam’iyyar labour party Julius Abure yace bai kamata a miƙa mulkin Najeriya a hannun shuwagabanni marasa lafiya ba a zaɓen 2023 mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar dai yayi wannan jawabi ne a ranar Asabar a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ta labour party da ya guda a garin lafiya babban birnin jihar Nasarawa dake Arewa ta tsakiyar Najeriya, The Cable ta wallafa.
Ɗan takarar mu lafiyayye ne
Ya bayyana cewa dukkanin matsalolin da ake fuskanta a yanzu a Najeriya suna da alaƙa da rashin nagartaccen shugabanci.
Ya ƙara da cewar ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar su wato Peter Obi lafiyayyen mutum ne, haka nan ya ƙara da cewar mataimakin Obi wato Datti Baba Ahmed shima mutum ne mai cikakkiyar lafiya.
“Ɗan takarar shugabancin ƙasar mu baya zuwa asibiti; mutum ne mai lafiya. Lafiyar shi ƙalau; haka nan ma mataimakin ɗan takarar mu ma lafiyar shi ƙalau.” inji shi.
Ya koka kan taɓarɓarewar abubuwa a Najeriya
Haka nan kuma ya koka kan yadda abubuwa suka taɓarɓare a ƙasar inda ya koka kan rashin tsaro da yayi ƙamari da kuma rashin aikin yi waɗanda sune suka dabai-baye ƙasar.
“A yanzu ƙasar tamu tana cikin hali na rashin lafiya. Tana fama da rashin lafiyar matsalar tsaro, tana fama da matsalar rashin aikin yi, haka nan tattalin arziƙin ƙasar baya gudana yadda ya kamata.
“Idan kuka haɗa waɗannan abubuwa guri guda zaku ga cewa ba zamu iya miƙa ƙasar nan ga marasa lafiya ba.” inji shugaban.
Ba mu son wanda zai riƙa kai mana kuɗaɗe waje
Daga ƙarshe ya bayyana cewa Najeriya na buƙatar lafiyayyen shugaba mai gaskiya wanda zai iya kwana bai barci ba wajen nemo ma ƙasar nan mafita ka halin da take ciki.
“Muna buƙatar jajirtacce, matashi, muna buƙatar mutane masu ƙwari waɗanda zasu iya hana idanunsu barci domin magance matsalolin ƙasar nan, kuma a yanzu haka mun samu irin wannan mutumin.
“Haka nan muna buƙatar wanda yake da tabbatacciyar gaskiya, wanda bazai riƙa kwasar kuɗaɗen mu yana kaiwa ƙasar waje ba. ” inji shugaban jam’iyyar.
Ana dai ganin cewa wannan shaguɓe da shugaban jam’iyyar keyi na da alaƙa da yadda shugaba mai ci ya riƙa zuwa ƙasar Birtaniya domin duba lafiyar sa da kuma jinyoyin da yayi fama dasu a baya.
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda yaro ɗan shekara 15 ya kashe mahaifiyar shi kan hana shi shaye-shaye.
Wani yaro ɗan shekara 15 dake zaune a ƙauyen Osubeng, gundumar Kwahu dake gabashin ƙasar Ghana ya kashe mahaifiyar shi sakamakon hana shi shaye-shaye da take yi.
Ance yaron mai suna Illiasu Amuni ya kashe mahaifiyar tashi mai suna Sakina Amuni ne dai ta hanyar buge ta da sanda sannan kuma ya yanka wuyan ta da wuƙa a yayin da take tsaka da aiki a gonar ta.
Wakilin majiyar mu ta Adom News wanda ya bibiyi labarin yadda abun ya samo asali ya bayyana cewa dama can baya yaron ya sha alwashin cewa lallai sai ya kashe mahaifiyar tashi saboda ta hana shi shaye-shayen tabar wiwi.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com