34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Yaro Dan shekara 15 ya kashe mahaifiyar shi kan hana shi shaye-shaye

LabaraiYaro Dan shekara 15 ya kashe mahaifiyar shi kan hana shi shaye-shaye

Wani yaro ɗan shekara 15 dake zaune a ƙauyen Osubeng, gundumar Kwahu dake gabashin ƙasar Ghana ya kashe mahaifiyar shi sakamakon hana shi shaye-shaye da take yi.

Yadda yaron ya kashe mahaifiyar tashi

Ance yaron mai suna Illiasu Amuni ya kashe mahaifiyar tashi mai suna Sakina Amuni ne dai ta hanyar buge ta da sanda sannan kuma ya yanka wuyan ta da wuƙa a yayin da take tsaka da aiki a gonar ta.

Wakilin majiyar mu ta Adom News wanda ya bibiyi labarin yadda abun ya samo asali ya bayyana cewa dama can baya yaron ya sha alwashin cewa lallai sai ya kashe mahaifiyar tashi saboda ta hana shi shaye-shayen tabar wiwi.

Ya amsa laifin da ya aikata

‘Yan uwan yaron dama sauran al’umma basu ɗauki barazanar da yaron yayi da muhimmanci ba har sai da yazo ya aikata wannan ɗanyen aiki.

A lokacin da ‘yan sanda suka iso, sun tasa ƙeyar wanda ake tuhuma inda ‘yan sandan suka ce ya amsa laifin shi na kashe mahaifiyar tashi.

Shugaban ƙauyen da wannan mummunan lamarin ya faru Nana Agyei Debrah Sasu yace kashe mahaifiyar shi da yaron yayi bai zo mishi da mamaki ba, sabili dama yaron ya taɓa yunƙurin sanya mata guba a cikin abinci.

Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ne sila

Nana Agyei dai ya alalaƙanta faruwar mummunan lamarin ga shaye-shayen miyagun ƙwayoyin da matasan suka duƙufa akai inda yayi kira ga iyaye akan su sanya idanun akan yaransu domin kauce ma faruwar irin hakan a gaba.

A wani labarin na daban kuma, kunji cewa Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Ruƙayya Umar Santa wacce aka fi sani da Ruƙayya Dawayya ta buɗe katafaren gurin gyaran jiki na mata a Kano.

Bikin ƙaddamar da wannan guri data buɗe ya samu halarta mutane da dama daga ciki da wajen masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood waɗanda suka zo don taya murna da kuma yin fatan alkhairi ga jarumar.

Jaruma Dawayya dai ta ƙaddamar da wannan katafaren guri ne dai data sanya ma suna ‘DY Utrat 85’ a ranar Laraba 26 ga watan Oktoban nan da muke ciki, a titin Guda Abdullahi dake Farm center a birnin Kano, kamar yadda Mujallar Fim ta wallafa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe