36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Wata mata ta maka uban ‘ya’yanta gaban kotu bisa zargin yayi mata fyade

LabaraiWata mata ta maka uban 'ya'yanta gaban kotu bisa zargin yayi mata fyade

Wata mata mai yara biyu ta maka mijin da zata aura kotu bisa zargin yayi mata fyade.

Matar ta maka mijin da za ta auran ne a wata kotu dake Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Matar wacce ta haifi yara biyu da wanda za ta aura din sannan ta kwashe shekaru suna rayuwa tare, na zargin shi da laifin yayi mata fyade shekara goma da suka gabata. Shafin LIB ya rahoto.

Suna rayuwa tare da wanda za ta aura

A takardar karar mai lamba UAC4/CA/322/2022/ wacce aka shigar ranar Juma’a 28 ga watan Oktoba, matar wacce take rayuwa tare da wanda zata aura a hanyar barikin sojoji, a Jimeta Yola, tace yayi mata fyade shekara goma da suka gabata lokacin da ta kawo masa abinci bayan ya bukaci da tayi hakan.

Tayi zargi a cikin karar cewa:

“Bayan mun fara soyayya ya kira ni a waya yace na dafa masa abinci na kawo masa saboda baya da lafiya. Yayi amfani da wannan damar yayi min fyade.”

Bayan ta kawo masa abincin, tayi ikirarin cewa ya sadu da ita ba tare da amincewar ta ba.

Bayan hakan ya auku ta samu juna biyu, lokacin da ta gaya masa tana da juna biyu sai yace sam ba na shi bane.

Bayan ta haihu ya yarda cewa jaririn na shi ne sannan ya nemi da ta yafe masa.

Daga nan sai suka fara rayuwa tare, inda ta kara samun wani juna biyun bayan wasu shekaru, sannan ta haifi  yaro na biyu.

Yunkurin ta na ganin ya aure ta ya ci tura

Tayi ta yunkurin ganin yaje ya gana da iyayenta domin suyi aure amma sai ya ki zuwa kwata-kwata.

A dalilin sa na kin yarda suyi aure da kuma rashin bata cikakkiyar kulawa ita da yaranta, matar ta maka shi a gaban kotu kan zargin laifuka uku.

Ta zarge shi da yi mata fyade, dukanta da yi mata barazana. Ta kuma zarge shi da nuna halin ko in kula wajen kulawa da ita da yaran su guda biyu.

Ana zargin cewa ta shigar da karar ne bayan ta fahimci cewa yana shirin korar ta daga gidan sa domin ya auro wata.

Mijin da za ta aura din dai ya musanta dukkanin zarge-zargen da take masa.

Mai shari’a Ibrahim Musa Ulenda, ya daga sauraron karar har sai ranar 1 ga watan Disamba, 2022

Wani babban fasto ya yiwa wata matar aure yayin yi mata addu’a

Wani babban fasto a wata coci a Rumuaholu a karamar hukumar Obio/Akpor, ta jihar Ribas, yayi wa wata matar aure fyade yayin yi mata adduar samun tsarkaka.

Wani mamba na wata kungiyar masu rajin kare hakkin biladama ta Center for Basic Rights and Accountability Campaign, Prince Wiro, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 10 ga watan Oktoban 2022

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana raayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe