Babban bankin Najeriya ya ce an yi zubar da kudade masu yawan biliyan 1.51 masu kimar Naira biliyan 698.48 a shekarar 2020, Legit.ng ta ruwaito.
An samu wannan rahoton ne a rahoton duk shekara da cibiyar gudanarwar kudade ta CBN ke saki duk shekara a ta shekarar 2020.
A Najeriya, CBN tana lalata kudaden da ba su dace a kashe su ba bisa tsatstsauran matakai wanda yayi daidai da dashi na 18(d) na dokar CBN ta shekarar 2007 wacce tilasta yin hakan.
Dokar ta tilasta lalata kudaden da ke yawo wadanda idan su ka je banki ba su da wani amfani kamar yadda sashi na 20(3) ya tanadar.
Kamar yadda CBN ta ruwaito, a shekarar 2020, an samu kudaden da yake yaduwa marasa kyau wadanda wajibi ne a lalata su don gabatar da sabbi.
A cewar CBN:
“A karshen watan Disamba na 2020, an samu kudade guda biliyan 1.51 (cikin akwatuna 151,427) masu kimar Naira miliyan 698,593.29. A shekara ta 2019 kusa an samu lalatattun kudi guda biliyan 1.57 (cikin akwatuna 157,217) masu kimar N814,437.60.
“An samu ragin akwatuna 5,790 da masu kimar N1,115.87 miliyan idan aka hada kudin 2019 da na 2020. Kuma ana zargin hakan yana da alaka da dakatar da siyayya na wani lokaci sakamakon annobar COVID 19 da ta barke.”
Saboda haka CBN ta bayyana cewa an yi amfani da Naira miliyan 538.59 wurin batar da lalatattun kudade a shekarar 2020, wanda a 2019 kuma an kashe Naira Miliyan 647.82 na yi hakan.
An samu ragin Naira miliyan 109.23 ko kuma kaso 16.86 bisa dari idan aka hada kudin da aka kashe wurin batar da kudaden a 2019.
Babban bankin Najeriya (CBN) zai sauya fasalin wasu daga cikin takardun kudin Naira
Babban bankin Najeriya (CBN) a ranar Laraba yace zai sauya fasalin takardar kudin N200, N500 da N1000.
Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, shine ya bayyana hakan a wani taron ganawa da manema labarai na musamman a birnin tarayya Abuja.
Sabon tsarin fasalin kudin zai soma aika daga 15 ga watan Disamban 2022. Rahoton Channels TV
A cewar gwamnan babban bankin an dauki wannan matakin ne domin a rage yawan kudin dake yawo a hannun mutane.
Shugaba Buhari ya amince da sauya fasalin takardun kudin
Godwin Emefiele ya bayyana cewa gwamnan ya samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin buga sabbin takardar kudin wanda za su maye gurbin na yanzu.
“A bisa tanadin sashin doka na 2(b) da sashin doka na 18(a) da sashin doka na 19, sakin layi na (a) da (b) na shekarar 2007, CBN ya nemi sannan ya samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin sake fasali, samarwa, saki da rarraba sabbin takardun kudin N200, N500 da N1000.” Inji shi
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com