Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Ruƙayya Umar Santa wacce aka fi sani da Ruƙayya Dawayya ta buɗe katafaren gurin gyaran jiki na mata a Kano.
Mutane da dama sun halarcin bikin buɗe gurin
Bikin ƙaddamar da wannan guri data buɗe ya samu halarta mutane da dama daga ciki da wajen masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood waɗanda suka zo don taya murna da kuma yin fatan alkhairi ga jarumar.
Jaruma Dawayya dai ta ƙaddamar da wannan katafaren guri ne dai data sanya ma suna ‘DY Utrat 85’ a ranar Laraba 26 ga watan Oktoban nan da muke ciki, a titin Guda Abdullahi dake Farm center a birnin Kano, kamar yadda Mujallar Fim ta wallafa.
An yaba ma Dawayya bisa ƙoƙarin da tayi
Mahalarta taron da dama sun yaba ma jaruma Dawayya bisa wannan yinƙuri data yi. Haka nan ma mutane da dama sun sayi wasu daga cikin irin kayayyakin da za’a riƙa saidawa a gurin a yayin bikin ƙaddamar wa.
Daga cikin mahalarta taro akwai Isma’il Na’abba Afakallahu, shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano. Akwai fitaccen jarumi Nura Hussaini, da su Hadizan Saima, Fauziyya Mai kyau, Hannatu Bashir, Saratu Gidado, Asma’u Sani da sauran wasu da dama daga ciki da wajen masana’antar ta Kannywood.
Da take jawabi jim kaɗan bayan ƙaddamar wa, jaruma Dawayya ta bayyana cewa dama ita ta daɗe tana sha’awar samar da gurin gyaran jiki da kuma kwalliyar mata, wanda a yanzu gashi ta cimma burinta.
Tsarin mu ya banbanta da irin na sauran gurare
Ta ƙara da cewa tsarin su ya banbanta da irin na sauran gurare domin sun samar da kayayyaki irin na ƙasashe daban daban don amfanin mutanen mu.
Dawayya ta ƙara da cewa basu tsaya iya ga kayyan kwalliya da gyaran jiki kaɗai ba, zasu riƙa haɗawa da kayayyakin amfanin yau da kullum na gida.
Da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamar wa, shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma’il Na’abba Afakallahu ya yaba da ƙoƙarin jaruma Ruƙayya Dawayya wajen buɗe irin wannan katafaren guri na gyaran jiki.
Afakallahu yace wannan abun a yaba mata ne duba da yadda tsarin gurin da ya kasance ta yanda zai kiyaye mutuncin mata. Sannan yaja hankalin mata akan su riƙa assasa sana’o’in da zasu riƙa kare mutuncin mata.
“Yanzu idan mu ka duba, wannan waje an tsara shi ne bisa kiyaye mutuncin duk wata mace da za ta zo wajen domin a yi mata gyaran jiki. Saboda yanayin tsarin wajen, mutum ko shi ya kawo matar sa, to sai dai ya ajiye ta ya tafi, don ba a yi wajen don mata ba. Ko da yake akwai wani ɓangare na gyaran jikin maza, amma dai ba a haɗe su ke ba.
“Don haka samar da irin wannan waje shi ne zai tabbatar da kiyaye mutuncin mu da na iyalan mu.” inji Afakallahu.
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda saurayi ya kashe budurwar shi kuma ya dafa wani bangare na naman jikinta.
‘Yan sanda a jihar Legas sun cafke wani mutumin mai suna Mayowa Dele ɗan kimanin shekaru 36 bisa tuhumar kashe budurwar shi tare da cire wasu sassa na jikinta.
Dailytrust ta ruwaito cewa yan sandan sunce a lokacin da suka kama saurayin, sun same shi yana ƙoƙarin dafa wasu sassa na jikin budurwar tashi da ya kashe.
Jami’in dake tuhumar mai laifin Thomas Nuruddeen, ya bayyana cewa abun da aka samu a cikin tukunyar da saurayin ya ɗora a wuta ya ƙunshi naman wasu sassa na jikin budurwar da aka kashe ne.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com