Wata mata mai suna Memphis Tennessee, wacce ake wa lakabi da Phi ta samu daukaka a kafar TikTok bayan wallafa bidiyo da hotunanta da yara 11 wadanda ko wannensu ubansa daban, Daily Mail ne ta ruwaito.
Wasu sun tausaya wa yaran inda har akwai masu zarginta da amfani da kudaden da iyayensu maza ke bata don kula da su wurin yin bishasharta yadda ta ga dama.
Sai dai Phi ta bayyana a wani bidiyo inda tace tana samun $10 duk wata don kula da ko wanne yaro kamar yadda kotu ta kayyade wa mazan.
A batun haihuwar yara da maza daban-daban, ta bayyana cewa idan da daya gare ta kuma mahaifinsa ya tsere ya bar ta ko kuma ya mutu, za ta rasa madafa.
Akwai wadanda ke zargin ta tara yaran ne don kawai ta dinga samun wani abu a hannun gwamnati.
Yanzu haka tana da mabiya fiye da 90,000 a TikTok kasancewar tana yawan wallafa bidiyonta tare da yaranta wadanda su ka yi kyau da kuma alamun ana kulawa da su.
Caccakar da ake yi mata ne ya sanya tayi bidiyo musamman don bayyana wa duniya dalilinta na daukar wannan mataki a rayuwarta da ta yaranta.
Yadda na haifi yara biyar tare da mahaifina bayan kwashe shekaru yana yi min fyade -Wata mata
Wata mata ta bayyana yadda mahaifinta ya kwashe shekaru yana yi mata fyade ita da kannenta mata.
Matar mai suna Aziza Kabibi tace mahaifinta ya fara yi mata fyade da bugunta lokacin da take da shekara 12 a duniya, inda tace tayi fatan dama ba ta zo duniyar nan ba. Shafin LIB ya rahoto.
Mahaifiyarta ba tayi komai ba a kai
Ta bayyana cewa mahaifiyarta tana sane da abinda mahafin nata yake mata amma ba tayi komai ba akai.
An hana ta zuwa makaranta sannan an ware ta daga cikin ‘yan’uwan ta don kada ta gayawa kowa abinda ake yi mata.
Matar ta kuma bayyana cewa mahaifin nata ya gaya mata cewa lalatar da yake da ita “umurnin ubangiji ne”
Tace ta so ta gudu ta bar gida a wani lokaci amma sai ‘yan’uwanta maza da mata suka hana ta.
Ta bayyana cewa ta fahimci idan ta bar gida, mahaifinta zai fara lalata da kannenta mata don haka sai ta tsaya. Mahaifinta yayi mata alkawarin cewa idan ta daina korafi, ba zai taba kannenta ba, don haka sai tayi shiru.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com