‘Yan sanda a jihar Legas sun cafke wani saurayi mai suna Mayowa Dele ɗan kimanin shekaru 36 bisa tuhumar kashe budurwar shi tare da cire wasu sassa na jikinta.
‘Yan sanda sun kama shi da sassan jikin budurwar tashi
Dailytrust ta ruwaito cewa yan sandan sunce a lokacin da suka kama saurayin, sun same shi yana ƙoƙarin dafa wasu sassa na jikin budurwar tashi da ya kashe.
Jami’in dake tuhumar mai laifin Thomas Nuruddeen, ya bayyana cewa abun da aka samu a cikin tukunyar da saurayin ya ɗora a wuta ya ƙunshi naman wasu sassa na jikin budurwar da aka kashe ne.
Thomas mai muƙamin mataimakin sufritandan ‘yan sanda ya shaida ma kotu cewar wannan mummunan lamari dai ya auku ne a titin Ijedodo da ke yankin Ijegun dake jihar Legas. Yace anan aka gano gawar matar mai suna Mercy.
Saurayin ya binne ta a wani kango
Ya ƙara da cewar akwai ƙarin wasu mutane uku da ake tuhuma kan sa hannun su a cikin aika-aikar. Ya bayyana sunan su da Oluwakemi Azeez ɗan shekara 20, Oyedegun Adewale ɗan shekara 27, da kuma Jejelaye Osusola ɗan shekara 22.
“Baya ga sanya wani ɓangare na jikin mamaciyar a tukunya, ya sanya wani a cikin wani buhun siminti da ya ɓoye a dakin shi, haka nan kuma ya nannaɗe sauran gangar jikin wacce ya binne ta a wani kango dake kusa da inda yake.” inji ɗan sandan.
‘Yan sandan sunce duk da har yanzu basu iya gano musabbabin yin kisan ba, ƙwararrun jami’ai daga cibiyar bincike ta jiha sun samu bayanai, wanda suka basu damar dira zuwa gidan wanda ake tuhuma, inda suka samo wasu sassa na jikin mamaciyar domin ya zama shaida.
Yace ba shi kaɗai yayi kisan ba
ASP Nuruddeen ya bayyana cewa wannan abubuwan da suka gano ne ya basu damar cafke babban wanda ake tuhuma, wanda daga nan ne aka riƙe shi domin ya amsa tambayoyi.
Ya ƙara da cewar a yayin da ake tuhumar mai laifin ne ya shaida wa ‘yan sanda cewa akwai wasu mutane uku da suka taimaka mishi wajen aiwatar da wannan aika-aika.
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda wani jami’in ɗan sanda mai suna ASP Abdullahi Garba ya kashe abokin aikin shi wani mai suna ASP Shu’aibu Sani Malumfashi har lahira sakamakon caka mishi almakashi da yayi biyo bayan wata ‘yar hayaniya data faru a tsakanin su.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar Kebbi DSP Nafi’u Abubakar yace ‘yan sanda sun samu saɓani ne sakamakon wata ‘yar turka-turka da ta faru tsakanin su a ƙofar shagon ɗan sandan da yayi kisan, kamar yadda Daily trust ta wallafa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com