24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Dan sanda ya kashe abokin aikin shi a Kebbi

LabaraiDan sanda ya kashe abokin aikin shi a Kebbi

Wani jami’in ɗan sanda mai suna ASP Abdullahi Garba ya kashe abokin aikin shi wani mai suna ASP Shu’aibu Sani Malumfashi  har lahira sakamakon caka mishi almakashi da yayi biyo bayan wata ‘yar hayaniya data faru a tsakanin su.

Sun samu saɓani a tsakanin su

Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar Kebbi DSP Nafi’u Abubakar yace ‘yan sanda sun samu saɓani ne sakamakon wata ‘yar turka-turka da ta faru tsakanin su a ƙofar shagon ɗan sandan da yayi kisan, kamar yadda Daily trust ta wallafa.

Jami’in ya ƙara da cewa Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi Ahmed Magaji Kontagora ya bada umarnin gudanar da bincike kan abubuwan da suka jawo faruwar lamarin.

Kwamishinan yayi Allah wadai da faruwar lamarin kuma ya bayyana cewa hakan ya saɓa da horo da kuma dokokin aikin ɗan sanda. Haka nan kuma yace hakan ya saɓa da da sauran dokokin ƙasar mu Najeriya.

Da almakashi ya kashe ɗan sandan

Wannan mummunan lamari dai ya faru ne a farkon wannan wata na Oktoba da muke ciki a sakamakon wata ‘yar hatsaniya da ta ɓarke tsakanin ASP Abdullahi Garba wanda ya caka ma abokin aikin shi Shu’aibu Sani Malumfashi a almakashi a haƙarƙarin shi na hagu.

Bayan samun labarin, DPO da ke kula da yankin Argungu, ya garzaya cikin gaggawa zuwa gurin da mummunan lamarin ya auku inda ya sanya aka kama ɗan sandan da yayi ta’adin tare da bada umarnin kai ASP Shu’aibu wani babban asibiti dake birnin Kebbi inda likita ya bayyana cewa ya rasu.

DPO ya bada umarnin kama mai laifin

Bugu da ƙari kuma, DPO ya bada umarnin kama ASP Abdullahi tare da iza ƙeyar shi zuwa babbar cibiyar tuhumar manyan laifuka ta ‘yan sandan jihar Kebbi, don gudanar da bincike.

A wani labarin na daban kuma, kunji cewa An buɗe wata cibiyar amfani da ruwan nono don maganin cututtuka a Amurka.

An buɗe guri na farko a duniya da za’a riƙa karɓa gami da tara madarar ruwan nono na mata a California dake ƙasar Amurka. Ƙwararru zasu gwada yiwuwar magance cututtuka da nonon da aka karɓa.

Cibiyar wacce aka buɗe ta a San Diego zata jaraba yin amfani da ruwan nonon matan wajen magance wasu manyan cututtuka da suka haɗa da ciwon zuciya, ciwon suga da kuma sankarar mama.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe