35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Ban ga amfanin barinta ba: Bayan yi masa ɗaurin rai da rai, mutumin ya datse mazakutarsa

LabaraiBan ga amfanin barinta ba: Bayan yi masa ɗaurin rai da rai, mutumin ya datse mazakutarsa

Wani mutum ya datse mazakutarsa bayan kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Mutumin mai suna Henry Hodges ya yanke wannan shawarar cikin bacin rai, LIB Ta ruwaito.

An yanke masa hukuncin ne bayan ya halaka wani mai gyaran waya a shekarar 1992. Ana zargin abinda ya hassala Henry shi ne yadda ya bukaci lauyansa ya kai masa abinci na alfarma a gidan yarin amma jami’ai su ka hana shi ci.

Da farko akan kisan da yayi, an yanke masa shekaru 40 ne, daga bisani kuma aka gane cewa shi ne ya halaka wani injiniya a wani otal da ke Atlanta.

Lauyansa ya kai masa ziyara Cibiyar Tsaro ta Riverbend Maximum a Nashville, inda ya je masa da abincin, sai dai an hana shi amsa.

An ga yadda Henry yayi bayan gida ya fara shafawa a bangon cikin gidan gyaran halin. Daga bisani kuma ya dauko reza a dakinsa inda ya fara yankar damtsensa a ranar 7 ga watan Oktoba.

Wani babban jami’i ya bukaci a mayar da shi daki bayan duba shi. Daga nan ne ya dauki reza a fasassun kwalabe inda ya guntule al’aurarsa gabadaya.

Yanzu haka jami’an sun samar da dakin da za a kebe shi a gefe guda, saboda kada ya zama hatsari ga kansa da wasu daban. Sannan kuma kada a dinga daure shi tamkar dabba.

Jami’an kwastam sun kama buhunhuna 16 makil da mazakutar jakai guda 7,000 ana shirin shillawa da su China

Jami’an hukumar kwastam sun yi ram da mazakutar jakai guda dubu bakwai, 7,000 da ake shirin yin sumogal din su zuwa Hong Kong, kasar China a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Jihar Legas, LIB ta ruwaito.

Shugaban kwastam din yankin, Sambo Dangaladima, wanda ya bayyana buhunhuna cike da mazakutar jakunan ya shaida yadda masu su su ka biya kudin da za a wuce da su kimanin N216,212,813.

A cewar Dangaladima, warin da buhununan ke yi ne ya janyo hankulan jami’an. Ya cigaba da cewa:

Masu kokarin fitar da su sun ce mazakutar shanaye ne. Amma bayan duba su dakyau aka gane cewa na jakai ne.

Wannan ne karo na farko da muka taba kwace wani abu mai kama da hakan. Ba za mu yarda ana irin wannan sana’ar a gabanmu ba.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe