Wata matar aure ‘yar kasar Ghana ta bayyana yadda ta ci amanar mijinta da direbanta wanda yanzu shine uban ‘ya’yanta.
Bayan ta kasa samun sukuni bisa abinda ta aikata, matar auren ta tonawa kan ta asiri inda ta bayyana yadda ta samu juna biyu sau biyu tare da direbanta.
Da take bayyana abinda ya faru, matar auren wacce aka sakaya sunan ta, tace aurenta da mijinta ya kai shekara shida, amma bata samu juna biyu ba. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Ta yanke shawarar zuwa ganin likita wanda yayi mata gwaje-gwaje inda ya gaya mata cewa babu wata matsala a tattare da ita.
Sai dai mijinta yaki zuwa domin a duba lafiyar sa.
Ta ci amanar aure tare da direbanta
Da take cigaba da bayar da labarin nata mai matukar kaduwa, matar auren ta bayyana cewa sai ta fara sakarwa direbanta fuska wanda ta bayyana a matsayin mutumin kirki.
Bayan alaka ta kullu a tsakanin su, sai suka bishe da yin lalata da juna inda har ta samu ciki. Bayan ta haifi yaron farko, ta kara samun wani juna biyun tare da direban.
Matar auren ta bayyana cewa direban ya san cewa yaran guda biyu na shine. Sai dai a daya bangaren kuma, mijinta bai san cewa yaran sa ba na shi bane.
Ga bidiyon nan kasa:
Mutane sun tofa albarkacin bakin su
Ernest Gyamfi ya rubuta:
“Zan rike su na kula da su a matsayin ‘ya’ya na. Mutane suna dauko yara su rike a matsayin yaran su.”
Kwetey Richard Tetteh ta rubuta:
“Wow abin birgewa, na ji dadi ta bayyana gaskiya.”
Yadda wani babban fasto yayi wa wata matar aure fyade yayin yi mata addu’ar tsarkakewa
A wani labarin na daban kuma, wani babban fasto yayi wa wata matar aure fyade yayin yi mata addu’ar tsarkakewa.
Wani babban fasto a wata coci a Rumuaholu a karamar hukumar Obio/Akpor, ta jihar Ribas, yayi wa wata matar aure fyade yayin yi mata addu’ar samun tsarkaka.
Wani mamba na wata kungiyar masu rajin kare hakkin bil’adama ta ‘Center for Basic Rights and Accountability Campaign’, Prince Wiro, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 10 ga watan Oktoban 2022
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com