36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

An buɗe cibiyar amfani da ruwan nono don maganin cututtuka

LabaraiLabaran DuniyaAn buɗe cibiyar amfani da ruwan nono don maganin cututtuka

An buɗe guri na farko a duniya da za’a riƙa karɓa gami da tara madarar ruwan nono na mata a California dake ƙasar Amurka. Ƙwararru zasu gwada yiwuwar magance cututtuka da nonon da aka karɓa.

Za’a yi amfani da ruwan nonon don magance cututtuka

Cibiyar wacce aka buɗe ta a San Diego zata jaraba yin amfani da ruwan nonon matan wajen magance wasu manyan cututtuka da suka haɗa da ciwon zuciya, ciwon suga da kuma sankarar mama, kamar dai yadda Daily mail ta wallafa.

Bincike da aka gudanar a shekaru da dama ya tabbatar da cewa ruwan nonon da ake shayar da ƙananan yara yana taimaka musu wajen ƙara musu kaifin basira, basu garkuwa ga lafiyar su, da kuma ƙara musu ƙarfin ƙashi. A dalilin haka ake so a gwada amfani da shi akan manyan domin aga irin gudummawar da zai bayar.

Darekatan hukumar, Lars Bode ya bayyana cewa akwai likitoci da sauran masu gwaje-gwaje da suka jaraba amfani da ruwan nonon a lokuta da dama a can baya.

63911145 11361491 image a 4 1666889489250

Masana daban-daban zasu gudanar da bincike akai

Ya ƙara da cewar kafa wanan cibiya da zata riƙa sarrafa ruwan nonon mata zai bada damar haɗuwa da masana daga fannoni daban-daban domin kaiwa ga matsaya guda ɗaya.

Ana sa ran dai cewa wannan cibiya da aka assasa a cikin jami’ar California dake San Diego, zata tattara masana daga ɗakunan gwaje-gwaje daban-daban waɗanda suka taɓa yin bincike akan yanayi, ƙarko da kuma magungunan da madarar nonon matan keyi a can baya.

63911157 11361491 image a 3 1666883640837

Babban maƙasudin assasa wannan cibiya dai shine domin jaraba yin amfani da madarar ruwan nono wajen magance cututtukan da suka addabi jarirai da kuma manya.

Masu binciken dai nason ganin yadda zasu yi amfani da ruwan maman wajen magance cututtukan da suka fi yawan addabar ƙananan yara.

Cibiyar na karɓar madarar nonon da mata ke zuwa suna badawa a kyauta. Bayan haka, ana fara gwada madarar, sannan a ɗan ɗumama, kafin daga bisani a sanya a cikin kwalebani inda anan ne ake duba wasu sinadarai dake ciki da kuma wasu ƙwayoyin halittu, kafin daga bisani a rarraba.

63911161 11361491 image a 3 1666889468186

Za’a taimaka wa matan da basu iya shayarwa

Ana kuma rarraba wata daga cikin madarar ruwan nonon da aka gama tantancewa zuwa asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya dabam-daban domin tallafawa mata masu ƙaramin ƙarfi da basu da isasshen nonon da zasu shayar.

A wani labarin na daban kuma, Tsohon ɗan dambe Emory Andrew Tate wanda kuma ya kasance mai faɗa aji a kafafen sadarwa na zamani ya bayyana shigar shi addinin musulunci.

Ya bayyana hakan ne dai a shafin shi na kafar sada zumunta ta zamani Gettr ranar Litinin. Duka kafafen sada zumunta na zamani in banda Gerttr sun dakatar da ɗan damben sakamakon yawaitar kalaman da yake yi waɗanda aka ayyana su a matsayin kalaman ƙin jinin mata.

A sanarwar da ya fitar, ya bayyana dalilin shi na karbar addinin musulunci, inda ya bayyana cewa duk wani Kirista da yayi yarda da kyawawan dabi’u sannan kuma ya fahimci yaƙi da munanan ɗabi’u to lallai dole ne ya musulunta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe