Yayin da yankuna da dama da ke cikin Jihar Kano ke fama da matsalar rashin wuta, samari da dama na gwagwarmayar ganin cewa sun kawo mafita saboda yadda ‘yan matansu su ka dena fito musu zance.
Anguwar Kuntau wani yanki ne da ke karamar hukumar Gwale a Jihar Kano, kuma tsawon lokaci tun da su ka shiga duhu har yanzu ba a samu mafita ba.
Daga cikin ‘yan matan yankin, ta shaida wa wakilin Dala FM yadda su ka dena fita zance soro saboda rashin wuta don za su cutu kwarai saboda sauro da duhu.
Akwai wadanda kuma wayoyinsu ne su ka mutu, hakan yasa su ka yanke alaka da samarin nasu duk da cewa ba haka rai yaso ba.
Tsofaffi kuwa har fita zanga-zanga su ka yi don ganin rashin dacewar duhun da aka sa su, don yanzu haka wasu ba sa samun damar bacci sai dare.
Tuni samari su ka zagara don ganin cewa sun kawo mafita akan wannan gagarumar matsalar da ke yunkurin raba su da ‘yan matansu.
Kawo yanzu dai KEDCO ba ta kawo sabuwar transformer ba, amma ana sa ran wannan koken zai yi aiki, ta yadda gwamnati ko kuma masu hannu da shuni za su duba wannan lamari don su kawo taimakon gaggawa.
Wani matashi ya hallaka dan uwan sa har lahira saboda rashin biyan kudin wutar lantarki
Wani matashi ya harbe yayan sa bisa rashin biyan kudin wutar lantarki a Uruagu, karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra, kudu maso gabashin Najeriya.
Ya zargi dan uwan sa da yanke masa wuta
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin, Peter Orji, ya zargi babban yayansa, Godwin Orji, da dage masa wutar lantarkin sa.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata.
Ya kasa biyan kudin wutan gidan sa
An dai ce wanda ake zargin ya kasa biyan kudin wutan bangaren sa har Naira 1,500 duk wata, wanda hakan ya sa wanda hakan ya tunzura wanda aka kashe ya yanke wutan gidan kanin nasa.
Wanda ake zargin ya fusata wanda hakan yasa ya tunkari dan uwan sa.
Rikici ya barke tsakanin ‘yan uwa biyu
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin ‘yan uwa biyu, wanda ake zargin ya afka dakinsa, tare da dauko bindiga ya harbe dan uwansa inda nan take ya ce ya ce ga garinku.
“Abinda ya faru shine tuntuni dama akwai ‘yar tsama tsakaninsu. Sun dade suna samun sabani a kan fili,” wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa PREMIUM TIMES.