24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Tsohon dan dambe da ya Musulunta ya bayyana dalilan sa

LabaraiTsohon dan dambe da ya Musulunta ya bayyana dalilan sa

Tsohon ɗan dambe Emory Andrew Tate wanda kuma ya kasance mai faɗa aji a kafafen sadarwa na zamani ya bayyana shigar shi addinin musulunci, the Islamic Information ta wallafa.

Kafafen sada zumunta sun dakatar da ɗan damben

Ya bayyana hakan ne dai a shafin shi na kafar sada zumunta ta zamani Gettr ranar Litinin. Duka kafafen sada zumunta na zamani in banda Gerttr sun dakatar da ɗan damben sakamakon yawaitar kalaman da yake yi waɗanda aka ayyana su a matsayin kalaman ƙin jinin mata.

A sanarwar da ya fitar, ya bayyana dalilin shi na karbar addinin musulunci, inda ya bayyana cewa duk wani Kirista da ya yarda da kyawawan dabi’u sannan kuma ya fahimci yaƙi da munanan ɗabi’u to lallai dole ne ya musulunta.

Tate ya koma Dubai da zama

Tsohon ɗan damben ɗan asalin ƙasar Birtaniya wanda yanzu haka yake zaune a haɗaɗɗiyar daular larabawa ya ƙarƙare sanarwar ta shi ne da rubuta aya ta ƙur’ani mai girma da take cewa “Lallai alƙawarin Allah gaskiya ne.”

Ana saura kwana ɗaya ɗan damben ya karɓi musulunci, an gan shi a wani faifan bidiyo yana koyon yadda ake yin sallah. Ance an ɗauki bidiyon ne a wani masallaci dake UAE, wanda ya karaɗe kafafen sada zumunta na Facebook da tuwita.

Tsohon ɗan wasan MMA Tam Khan ne dai ya ɗora bidiyon a shafin Facebook ɗin sa wanda ya bayyana cewa shi ya ɗauki bidiyon wanda yake nuna cewa Tate ya karɓi kalmar shahada.

Ya shahara saboda da yawan cece-kuce

Andrew Tate wanda yafi shahara a can baya saboda wasan damben da yake yi. Ya samu ƙarin shuhura ne a shekarar 2022 sabili da maganganun da yake yi akan mata waɗanda wasu ke ganin kamar kalamai ne na ƙin jinin mata.

Daga cikin irin kalaman da mutane suka soke shi sosai akwai kalamin da yayi na cewar babu inda ya fi dacewa da bata face gidajen su. Kada mata su tuƙa mota, kuma su mata gaba ɗayansu mallakin mazaje ne.

Sakamakon yawan maganganun da yake waɗanda ke tada ƙura, an rufe mishi shafukan shi dake kan kusan duka kafofin sada zumunta na zamani da suka haɗa da Facebook, Twitter, Instagram, YouTube, Tiktok da dai sauransu.

A wani labarin na daban kuma, kunji yadda sojojin Amurka da jami’an farin kaya suka kama ‘yan ta’adda a Abuja.

Jami’an farin kaya tare da haɗin gwuiwar sojojin Amurka sunyi nasarar cafke wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne su biyu a rukunin gidajen Trademore dake yankin Lugbe dake birnin tarayya Abuja.

Ance jami’an tsaron sun toshe hanyar shige da fice na unguwar a yayin da suka gudanar da samamen da suka kama wasu mutane biyu da ake zargi da ta’addanci.

Jaridar The cable ta wallafa cewa shugaban unguwar Adewale Adenaike ya bayyana ma manema labarai yadda jami’an tsaro na farin kaya tare da haɗin gwuiwar wasu sojojin Amurka suka shigo unguwar gami da kama wasu mutane biyu a yankin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe