24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Yadda wani jami’in dan sanda ya halaka abokin aikin sa har lahira a jihar Kebbi

LabaraiYadda wani jami'in dan sanda ya halaka abokin aikin sa har lahira a jihar Kebbi

Hukumar ‘yan sandan jihar Kebbi ta sanar da cewa daya daga cikin jami’anta mai suna ASP Abdullahi Garba ya halaka abokin aikin sa mai suna ASP Shuaibu Sani Malumfashi, wanda hoton sa ke a kasa. 

635ab93226345 2
Hoton marigayi ASP Shuaibu Sani Malumfashi. Hoto daga LIB

Kakakin hukumar ‘yan sandan na jihar, SP Nafiu Abubakar, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa  ranar Alhamis 27 ga watan Oktoba 2022, yace kwamishin ‘yan sandan jihar ya bayar da umurnin a gudanar da kwakkwaran bincike domin gano hakikanin yadda lamarin ya auku. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

An bayyana abinda ya faru tsakanin su

A cewar kakakin, ASP Garba ya cakawa ASP Malumfashi almakashi ne a yayin wata hatsaniya a garin Argungu a ranar 19 ga watan Oktoba, 2022. 

An garzaya da ASP Malumfashi asibiti cikin gaggawa a Birnin Kebbi, inda likita ya tabbatar da cewa ya rasu.

“A ranar 19 ga watan Oktoba 2022, da misalin karfe 2:10 na rana, wani jami’i ASP Abdullahi Garba, mai kula ofishin ‘yan sanda na Sauwa, ya samu hatsaniya da ASP Shuaibu Sani Malumfashi, jami’i a babban ofishin ‘yan sanda na Argungu, a wurin kamun kifi na Argungu.”

“A dalilin hakan sun ba hammata iska a gaban shagon Abdullahi Garba. A lokacin da suke fadan, ASP Abdullahi Garba yayi amfani da almakashi ya cakawa ASP Shuaibu Sani Malumfashi, a harkakarin sa.” A cewar sanarwar.

Kafin rasuwar sa marigayi ASP Malumfashi yana aiki ne a ofishin ‘yan sanda na Argungu a jihar Kebbi.

Kakakin ya kuma bayyana cewa jami’in dan sandan da ya aikata laifin an sakaya shi a ofishin ‘yan sanda yayin da ake cigaba da gudanar da bincike.

Yadda dan sanda ya bindige abokin aikin sa bayan gardama ta barke a tsakanin su

A wani labarin na daban kuma, wani jami’in dan sanda ya bindiga get abokin aikin sa har lahira a jihar Abia.

Hukumar ‘yan sandan jihar Abia ta bayyana cewa ta cafke wani jami’in dan sanda bisa bindige abokin aikin sa.

Dan sandan da aka halaka mai suna Samuel Ugor, wanda Insufeta ne, an bindige shi ne bayan gardama ta barke a tsakanin su.

Da yake bayani a wani taron manema labarai, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Godfrey Ogbonna, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin a babban birnin jihar Umuahia.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe