34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Yadda sojojin Amurka da jami’an farin kaya suka kama ‘yan ta’adda a Abuja

LabaraiYadda sojojin Amurka da jami'an farin kaya suka kama 'yan ta'adda a Abuja

Jami’an farin kaya tare da haɗin gwuiwar sojojin Amurka sunyi nasarar cafke wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne su biyu a rukunin gidajen Trademore dake yankin Lugbe dake birnin tarayya Abuja.

Ance jami’an tsaron sun toshe hanyar shige da fice na unguwar a yayin da suka gudanar da samamen da suka kama wasu mutane biyu da ake zargi da ta’addanci.

Jami’an farin kaya da sojojin Amurka ne suka yi aikin

Jaridar The cable ta wallafa cewa shugaban unguwar Adewale Adenaike ya bayyana ma manema labarai yadda jami’an tsaro na farin kaya tare da haɗin gwuiwar wasu sojojin Amurka suka shigo unguwar gami da kama wasu mutane biyu a yankin.

Ya ƙara da cewar jami’an tsaron da suka zo sun shaida mishi cewa suna neman wasu mutane da suke zargin suna da alaƙa da ayyukan ‘yan ta’adda.

“Lamarin dai ya faru ne ranar Litinin data gabata. Muna a cikin gidajen mu a lokacin da aka rufe hanyar shigowa unguwar tamu. Ba’a barin kowa ya shigo, haka nan ba’a barin kowa ya fita daga cikin unguwar tamu.

Shugaban yankin ya bada bayani

“Na fito a matsayina na shugaban yankin domin na ji ko menene ke faruwa a yankin. Sai nake samun labarin cewa wani atisaye ne na musamman jami’an farin kaya da kuma wasu sojojin Amurka.

“Ance wai suna neman wani mutum ne da yake da alaƙa da ayyuka na ta’addanci, amma bani da tabbaci kan hakan.” inji Adewale.

Ya ƙara da cewar a lokacin da ya tunkari ƙofar shiga unguwar da zummar ya fita ya zuwa layin da yake zama sai jami’an farin kaya suka tsaida shi. Ya nuna musu cewa shine shugaban yankin, kuma mutane na ta kiran shi a waya domin suji ko me ke faruwa.

Jami’an tsaron sun bayyana mishi cewa suna neman wani da suke zargin yana da alaƙa da ‘yan ta’adda ne.

Yace bayan da suka gama abinda zasu yi, sun gan jami’in farin kayan da kuma sojojin na Amurka sun tafi da wasu mutane a cikin motocin su.

‘Yan ta’adda na yunkurin kai hari Abuja

A kwanakin baya ne dai hukumomin ƙasashen Amurka da na ƙasar Birtaniya suka gargaɗi ‘yan kasashen su dangane da tafiya zuwa babban birnin tarayya Abuja. Sun musu wannan gargaɗi ne dai saboda bayanan da suka ce sun samu kan yiwuwar samun hare-haren ‘yan ta’adda a Abuja.

A wani labarin na daban kuma, kunji wani magidanci da ya maka matar shi wata kotu dake Nyanya Abuja bisa ƙorafin cewa ta ƙi ta bayyana mishi ko nawa take amsa a matsayin albashin ta.

Majiyar mu ta wallafa cewa mijin ya bayyana cewa matar ba ta yi mishi biyayya kuma ta kasance mai yawan tafiye-tafiye ba tare da tana sanar dashi ba a duk lokacin da zata yi tafiya.

Ya bayyana ma kotu cewa ya kamata ace a duk lokacin da matar zata je wani guri ta zamto tana sanar dashi a matsayin shi na mijin ta kuma shugaban gidan. Amma sai dai matar kawai ta fita a duk lokacin da ta gama.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe