Dan kasar Chanan nan Geng Quangron da ake tuhumar sa da kisan budurwar sa ‘yar Kano, Ummulkulsum Sani Buhari wacce akafi sani da Ummita ya musanta aikata laifin zargin da ake tuhumar sa da shi.
Mista Geng ya bayyana hakan ne a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 17 da ke a Miller Road, yayin da kotun ta ci gaba da sauraren karar da Gwamantin Jihar Kano ta shigar tana zargin sa da kisan Ummulkusum. Rahoton jaridar Aminiya.
Ana dai zargin Mista Geng da kisan Ummita, wacce ta kasance suna soyayya da juna, inda ya bita har unguwar su dake Janbulo ya shiga har cikin gidansu ya caccaka mata wuka, wanda hakan yayi sanadiyyar rasa ranta har lahira.
An nemo wanda zai yi masa fassara
A baya an sami tsaiko a sauraren shari’ar sakamakon rashin wanda zai yiwa wanda ake zargi fassara, bisa la’akari da cewa yana daga cikin hakkinsa a yi masa sharia da harshen da ya fi fahimta.
A zaman kotun na ranar Alhamis, mai gabatar da kara, Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Barista Musa A. Lawan ya gabatar wa kotun wanda zai yi aikin fassarar wanda kuma dan asalin kasar Chana ne mai suna Mista Guo Cumru.
Takardar da mai gabatar da kara ya karanta na cewa:
“A ranar 16 ga watan Satumba, kai Mista Geng da ke zaune a rukunin gidajen da ke unguwar Railway a jihar Kano ka je wani gida a unguwar Janbulo a Jihar Kano inda ka kashe wata budurwa mai suna Ummulkusum Sani Buhari ta hanyar caccaka mata wuka a wurare daban-daban na jikinta.”
“Laifin da ake zargin ka da aikatawa dai ya saba da sashe na 221 a cikin kundin Pinal Kod.”
Sai dai Mista Geng Quanron ya musanta aikata laifin da ake zargin sa da shi.
An bukaci a daga sauraron karar
Mai gabatar da kara ya nemi kotun da ta daga shari’ar zuwa ranar 14 zuwa 16 ga watan Nuwamba don su gabatar da shaidunsu.
Sai dai lauyan wanda ake tuhuma Barista Muhamamd Balarabe Danazumi bai amince da wannan ranaku ba, inda ya shaida wa kotu cewa ranakun ba su yi masa daidai ba.
Sai dai mai gabatar da kara ya roki kotun da ta yi la’akari da cewa mai yin fassarar yana zuwa ne daga birnin tarayya Abuja.
Alkalin kotun, mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji, ya dage shari’ar zuwa ranar 16 da 17 da 18 ga watan Nuwamban 2022.
Yadda dan Chana ya yaudari Ummita cewa ya musulunta -Babbar kawarta
Wata ƙawar Ummukulsum Sani Buhari (Ummita) matashiyar nan da Geng Quanrong ya halaka a Kano, ta bayyana cewa ya yaudari marigayiyar da cewa ya musulunta domin ta aure shi.
Daily Trust ta rahoto cewa Quanrong yanzu haka yana garƙame a hannun ƴan sanda bisa halaka Ummita a gidan iyayenta a ranar Juma’a. Ummita da Quanrong masoya ne
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com