LabaraiIna alfahari da cika shekaru 14 da aure ba...

Ina alfahari da cika shekaru 14 da aure ba tare da an ji kanmu matata ba, Jaruma Lawan Ahmad

-

- Advertisment -spot_img

Fitaccen jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywood, Lawan Ahmad ya bayyana cewa a zamansu da matarsa, Saratu Abdulsalam, babu wani ya taba kai karar wani tsawon shekaru 14 da aure.

Mujallar Fim ta zanta da jarumin inda yace yana matukar farinciki tare da alfahari da cika shekaru 14 a ranar 25 ga watan Oktoban 2022, ba tare da an ji kansa da matarsa ba.

Ya wallafar zazzafan hotonsa tare da uwar ‘ya’yansa don murnar. Yayin tattaunawa da Mujallar Fim, jarumin ya ce:

Alhamdulillah, ina farinciki tare da alfahari da Allah cikin ikonsa yasa mu ka cika shekaru 14 da aure. Kuma babu wani a cikinmu da ya taba kai karar wani gidan iyayensa. Mu na zaune da dadi babu dadi, har mu ka cika shekarun nan.

Tabbas ba karamin abin alfahari ba ne wannan, kuma ba karamar ni’ima bace da Allah yayi mana tsawon shekarun nan. Gaskiya ina matukar farinciki.”

Lawan yana daya daga cikin ‘yan fim wadanda babu wanda ya taba jin wani mummunan labari tsakaninsa da matarsa duk da yadda jama’a ke kallon ‘yan fim ba sa rike aure.

Yayin da aka tambayeshi ko zai yi karin bayani, ya bayyana cewa:

Babu wanda ba ya zaman aure. Dama idan har aka yi aure akwai saki, kuma addini ma ya amince da hakan. Kowa ya riga ya sani. Kuma dalilin da yasa ake ganin kamar ‘yan fim ba sa zaman aure, saboda komai nasu a bude yake.

Ya bayyana cewa da zarar dan fim ya bayyana wani abu ko ya wallafa shi, nan da nan mutane za su dauka su ci gaba da yadawa. Hakan ya biyo bayan yadda kowa ya san su.

An tambayeshi idan yana da burin kara aure, sai ya kada baki yace, “shi aure zuwa yake yi. Don haka babu wani zabi sai abinda Allah ya tabbatar mana.” Yanzu haka yaran da Allah ya azurta su da su guda hudu ne, akwai Ahmad, Aliyu, Fatima da Habiba.

Kokarin tsige Buhari: APC ta ba wa Ahmad Lawan mako 2 ya yi murabus

Wata kungiya ta jam’iyyar APC, ta ce ta gano shirin da wasu ‘yan majalisu na tarayya ke yi wdomin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari. Haka kuma kungiyar ta bukaci shugaban majalisar dattawa na kasa Sanata Ahmad Lawan da ya yi murabus daga kujerarshi bayan zargin shi da hannu a wannan yunkuri na tsige shugaban kasar.

A rahoton da jaridar Blueprint ta fitar, kungiyar ta bayyana tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima da kuma wasu Sanatoci daga jam’iyyar adawa a matsayin wadanda za a bincika kan wannan lamari.

Wannan dai ya fito a wata sanarwa da kungiyar ta fitar ga manema labarai ta bakin sakataren yada labarai, Alhaji Bala Abubakar, wanda ya zargi wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar APC da hada kai da ‘yan jam’iyyar adawa domin biya wasu bukatunsu na son rai.

Abubakar ya ce: “Mun gano cewa akwai wasu baragurbi a cikin mu da suka hada kai da ‘yan jam’iyyar adawa domin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari su maye gurbinshi da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda suke so ya kammala wa’adin shugaban kasar na shekara biyu.

“Ba za mu taba yadda da irin wannan abu ba da ‘yan jam’iyyar APC suke shirin yi.

“Wannan wani shiri ne na bata tsarin dimokuradiyyar Najeriya, sannan kuma a kara kawo wata matsalar a cikin al’umma. Baza muyi kasa a guiwa ba wajen bin duk wata hanya da zamu hana wannan abu faruwa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: labarunhausa@labarunhausaagmail-com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su ka lamushe wiwi mai nauyin 200kg bayan sun kwace ta...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama shi sannan a sakaya shi saboda ya lakada mata na...

Wata mata ta haihu a masallacin Annabi

Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma'aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu...

‘Yan gida daya su 11 sun mutu bayan cin wani abinci

Aƙalla mutane 11 ne 'yan gida ɗaya aka tabbatar da sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargin...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Matashi ya kaɗu bayan gano cewa budurwar sa a kango take rayuwa

Wata matashi ɗan Najeriya ya shiga kaɗuwa matuƙa bayan gano cewa budurwarsa ta tsawon wata takwas a cikin wani...

An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka

Nabeela Syed, 'yar asalin ƙasar Indiya ta kasance mace musulma ta farko da aka zaɓa a matsayin 'yar majalissar...

Must read

Ɓeraye ne su ka bushe wiwin da mu ka ƙwace mai nauyin 200kg, ‘Yan sanda

‘Yan sandan Indiya sun koka kan yadda beraye su...

Daɗi miji: Bayan an kulle shi saboda ya laƙada mata duka, matar ta yi belin mijinta

Wata mata ta yi belin mijinta bayan an kama...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you