Wani magidanci mai suna Gyang Gyan ya maka matar shi mai suna Jemima a wata kotu dake Nyanya Abuja bisa ƙorafin cewa ta ƙi ta bayyana mishi ko nawa take amsa a matsayin albashin ta.
Matar bata yi mishi biyayya
Majiyar mu ta Dailytrust ta wallafa cewa mijin ya bayyana cewa matar ba ta yi mishi biyayya kuma ta kasance mai yawan tafiye-tafiye ba tare da tana sanar dashi ba a duk lokacin da zata yi tafiya.
Ya bayyana ma kotu cewa ya kamata ace a duk lokacin da matar zata je wani guri ta zamto tana sanar dashi a matsayin shi na mijin ta kuma shugaban gidan. Amma sai dai matar kawai ta fita a duk lokacin da ta gama.
Bata sanar dani in zata fita
“A matsayi na na maigida, ya kamata ace matata tana sanar dani a duk lokacin da zata je wani gurin, amma kawai ta na fita a duk lokacin da taga dama ba tare da sanar dani ba.”
Ya kuma ƙara da cewar matar bata neman iznin shi ko kaɗan a yayin fita. Kuma bata ganin girman shi, bata bin umarnin shi a gidan, tana yin abinda kawai taga dama ne.
“Ina gane tayi tafiya ne kawai idan na ƙyalla ban ganta a gida ba. Bata bin umarni na kuma bata mutunta ni.”
Hakanan kuma mijin ya ƙara shaida ma kotun cewa matar bata taimaka mishi a harkokin gida, ta bar dawainiyar gida da sauran kwaranniyoyin yara duka a hannun shi.
Ina fama da ciwon hawan jini
Sannan mijin ya ƙara bayyana ma kotu cewa yanzu haka yana fama da ciwon suga da hawan jini, amma duk da haka matar taƙi ta bayyana mishi ko nawa ne albashin da take samu.
“Mata ta bata taimaka mini, ta bar dawainiyar yara duka a hannuna.
“Yanzu ina fama da ciwon suga da kuma hawan jini. Amma matar ta ƙi ta bayyana min ko nawa ne take karɓa a matsayin albashin ta.”
A dalilin haka, mijin ya roƙi kotu da ta raba auren nasu kafin hawan jini ya kashe shi saboda baƙin ciki.
Sai dai kuma matar wacce ita ce ake tuhuma ta musanta ƙorafe-ƙorafen da mijin nata yake yi.
A nashi ɓangaren, alƙalin kotun Doocivir Yawe ya buƙaci ma’auratan da suyi haƙuri suje su sulhunta kansu duba da yawan shekarun da suka kasance a tare a matsayin ma’aurata.
“Kun kasance a tare sama da shekara 27. A wannan matakin da ya kamata ace zaka more lokacin ritayar ka tare da iyalanka amma kuma yanzu kuna ƙoƙarin kotu ta raba auren naku. Kuyi ƙoƙarin zuwa kuyi sulhu kafin a zartar da hukunci.” inji alƙalin.
A wani labarin kuma, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya Kuma tsohon ɗan takarar kujerar gwamna a jihar Kaduna Kwamared Shehu Sani ya yi martani game da batun sauya fasalin kuɗaɗe da gwamnatin tarayya ke shirin yi.
Shehu Sani yayi martanin dai a shafin shi na tuwita jim kaɗan bayan fitar sanarwar da babban bankin Najeriya ya fitar kan cewa nan ba da jimawa ba za’a sauya fasalin wasu daga cikin takardun kuɗaɗen da muke amfani da su.
Kwamared Shehu Sani ya bayyana a shafin shi na tuwita cewa dalilin da ya sa Buhari ya canja kuɗi a lokacin da yayi mulkin soja wato a shekarar 1984, shine dalilin da ya sanya Buhari zai sauya fasalin kuɗin ma a yanzu.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com