Shehu Sani yayi martanin a shafin shi na tuwita
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya Kuma tsohon ɗan takarar kujerar gwamna a jihar Kaduna Kwamared Shehu Sani ya yi martani game da batun sauya fasalin kuɗaɗe da gwamnatin tarayya ke shirin yi.
Shehu Sani yayi martanin dai a shafin shi na tuwita jim kaɗan bayan fitar sanarwar da babban bankin Najeriya ya fitar kan cewa nan ba da jimawa ba za’a sauya fasalin wasu daga cikin takardun kuɗaɗen da muke amfani da su.
Dalilin ɗaya ne da na 1984
Kwamared Shehu Sani ya bayyana a shafin shi na tuwita cewa dalilin da ya sa Buhari ya canja kuɗi a lokacin da yayi mulkin soja wato a shekarar 1984, shine dalilin da ya sanya Buhari zai sauya fasalin kuɗin ma a yanzu.
Tsohon sanatan ya bayyana cewa dalilin da yasa Buhari zai sauya fasalin kuɗin shine saboda halin matsi da taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa da ake ciki.
Ana fargabar cire ajamin larabci.
Wasu mutanen kuma suna ganin ba wannan bane dalilin da yasa ake ƙoƙarin sauya fasalin kuɗaɗen. Mutane da dama nada saɓanin ra’ayi da Shehu Sani akan batun. Akwai waɗanda suka yi fargabar cewa za’a iya cire rubutun ajamin larabci dake jikin kuɗaɗen.
A ranar Larabar nan ne dai gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya fitar da sanarwar cewa babban bankin Najeriya na shirin fito da sababbin kuɗaɗen N200, N500 da kuma N1,000 masu sabon fasali daga ranar 15 ga watan Disamba.
Daga dalilan da aka bada na kawo sababbin nau’in kuɗaɗen akwai magance matsalar ta’ammuli da yagalgalallun kuɗaɗe masu datti, hakanan kuma za’a samu sauƙi sosai wajen daƙile masu buga kuɗaɗen jabu.
Gwamnan ya ƙara da cewa sababbin fasalin kuɗaɗen zasu ƙara taimakawa wajen daƙile biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane. Sai dai kuma yace duk wanda zai ajiye kudi a banki da suka kai N150,000 to za’a caje shi wani abu, wanda hakan zai kara taimakawa wajen samun kuɗaɗen shiga.
A wani labarin kuma, Wata babbar kotun jihar Kano ta yankewa wani matashi mai suna Aminu Ishaq hukuncin shekara uku a gidan kaso bisa amfani da kudin haram.
Alkali mai shari’a Nasiru Saminu shine ya zartar da wannan hukuncin a ranar 25 ga watan Oktoban 2022.
Matashin da aka yankewa hukuncin yana daya daga cikin matasa shida da aka cafke a satar sama da Naira miliyan sha biyar (N15,000,000m) daga asusun wata tsohuwa wacce kaka ce ga daya daga cikin su (Al-Mustapha Nasir).
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com