24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Babban bankin Najeriya (CBN) zai sauya fasalin wasu daga cikin takardun kudin Naira

LabaraiBabban bankin Najeriya (CBN) zai sauya fasalin wasu daga cikin takardun kudin Naira

Babban bankin Najeriya (CBN) a ranar Laraba yace zai sauya fasalin takardar kudin N200, N500 da N1000.

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, shine ya bayyana hakan a wani taron ganawa da manema labarai na musamman a birnin tarayya Abuja.

Sabon tsarin fasalin kudin zai soma aika daga 15 ga watan Disamban 2022. Rahoton Channels TV

A cewar gwamnan babban bankin an dauki wannan matakin ne domin a rage yawan kudin dake yawo a hannun mutane.

Shugaba Buhari ya amince da sauya fasalin takardun kudin

Godwin Emefiele ya bayyana cewa gwamnan ya samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin buga sabbin takardar kudin wanda za su maye gurbin na yanzu.

“A bisa tanadin sashin doka na 2(b) da sashin doka na 18(a) da sashin doka na 19, sakin layi na (a) da (b) na shekarar 2007, CBN ya nemi sannan ya samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin sake fasali, samarwa, saki da rarraba sabbin takardun kudin N200, N500 da N1000.” Inji shi

“A bisa samun wannan amincewar, mun kammala shirye-shiryen domin fara raba sabbin takardun kudin daga ranar 15 ga watan Disamban 2022, bayan shugaban kasa ya kaddamar da su.

“Sabbin takardun kudin da wadanda ake amfani da su yanzu, za su cigaba da aiki tare har zuwa 31 ga watan Janairun 2023, lokacin da takardun kudin na yanzu za su daina aiki.”

Da zarar an kammala buga sabbin takardun kudin, ‘yan Najeriya za su iya zuwa bankuna da tsaffin takardun kudin domin amsar sabbi.

CBN ya damu kan kudin dake yawo a hannun mutane

Gwamnan babban bankin Najeriya ya nuna damuwar sa kan yadda ake ajiye kudin Najeriya yanzu haka.

A cewar sa, mafi yawan takardun kudin kasar nan basa ajiye a bankuna, wanda hakan abu ne wanda babban bankin ba zai lamunta ba.

CBN ya umurci bankuna da su gwangwaje ‘yan Najeriya da kudade a asusun ajiyar su

Biyo bayan ƙara yawan kuɗin ruwa zuwa kaso 15.5% da babban bankin Najeriya (CBN), yayi, bankin ya umurci bankuna da riƙa biyan kaso 4.65% na kuɗin ruwa kan asusunan ajiya na banki, hakan yasa an samo ƙarin kaso 4.2% kan wanda bankunan ke biya a baya.

Wannan umurnin na zuwa ne bisa ƙarin da akayi na tsarin farashin kuɗi zuwa kaso 15.5% daga kaso 14%. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe