Ɗalibar na kan hanyar zuwa gida
Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba’a iya gano ko suwa ne ne ba sun harbe wata ɗalibar aikin lafiya wacce aka bayyana sunan ta da Celestina wacce tayi karatun likitanci a jami’ar Ambrose Alli dake Ekpoma jihar Edo.
Wannan lamari dai ya faru ne a yayin da ɗalibar ke dawowa daga wajen bikin ƙaddamar dasu zuwa aikin lafiya da ya gudana a farfajiyar makarantar dake Ekpoma kan hanyar ta ta zuwa gidan iyayen ta dake Abuja, kamar yadda majiyar mu ta Yabaleft ta wallafa.
Kwana 13 da ƙaddamar dasu a aikin lafiya
Wannan mummunan lamarin dai na zuwa ne kwana goma sha uku da ƙaddamar da ɗalibar cikin aikin lafiya ɓangaren gwaje-gwajen cututtuka ta ƙasa.
Kafin mutuwar wannan ɗaliba, ta riƙe muƙamai da dama a yayin da take makaranta. Daga ciki akwai, mataimakiyar shugaban ɗaliban katolika masu karantar aikin likitancin jinya da kuma na likitocin haƙori.
Sai dai kuma wasu na ganin mutuwar nada alaƙa da aikin ‘yan ta’adda da suka yawaita akan hanyoyin ƙasar nan waɗanda suke cin karen su ba babbaka akoda yaushe.
Mutane sun nuna alhininsu
Mutane da dama musamman a kafafen yaɗa labarai na zamani sun nuna alhininsu gami da jajanta ma ‘yan uwan ɗalibar bisa wannan mummunan lamari da ya faru.
A wani labarin kuma, kunji yadda wasu matasa ‘yan luwadi suka kashe kansu ta hanyar fadowa daga kan gada.
Wasu matasa ‘yan luwaɗi su biyu sun kashe kawunan su ta hanyar faɗowa daga kan wata gada mai tsayi bayan sun sumbaci junan su.
Matasan da aka bayyana sunan su da Tigran da kuma Arsen dai sun yaɗa wasu hotuna nasu suna sumbatar juna a shafin Instagram, tare da rubuta cewa suna murna da kawo ƙarshen rayuwar su. Kuma wannan matakin da suka ɗauka su biyun duka sun amince da shi.
Gama hakan keda wuya sai kawai matasan suka sulmiyo ƙasa daga kan gadar Davtashen mai tsawon tako 31 wacce take a Yerevan, babban birnin ƙasar Armeniya kamar yadda majiyar mu ta NY Times ta wallafa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com