William Getumbe, fitaccen mawakin yabon addinin kirista ya bayyana cewa yana yin fitsarin kwance idan har ya kwanta bacci, da kuma yadda yake dawainiya da lalurar, Legit.ng ta ruwaito.
Yayin tattaunawar da su ka yi da Jaridar Kenya ta TUKO.co.ke, mawakin ya bayyana cewa matarsa Virginia Masitha ta san halin da yake ciki sannan ita ce ma take yi masa kunzugu ko wanne dare kafin su kwanta.
Lalurar fitsarin kwance ba sabuwar lalura bace kuma tana faruwa da zarar mutum ya kwanta yana bacci ba tare da sani ba ya fara fitsari. A cewar Getumbe, akwai manya da dama da ke fitsarin kwance amma su na jin kunyar bayyana wa duniya.
Ya ce hakan ya yi matukar raba auren jama’a da dama. Mawakin yabon Yesun ya yaba wa matarsa akan kokarin da take yi dangane da shi da lalurarsa inda take ji da shi tamkar jariri a ko wanne dare.
“Akwai aure da dama da ya mutu saboda fitsarin kwance. Saidai matata ta fahimceni fiye da tunani inda take yi min kunzugu a ko wanne dare ba tare da raina ni ba,” inji shi.
Getumbe ya shawarci duk masu lalurar fitsarin kwance musamman maza masu iyalinda su dinga yin kunzugu kafin su kwanta don gudun yin shi a gado.
Ya ci gaba da cewa:
“Akwai maza da dama da ke amfani da kunzugu kamar masu zuwa makaranta, ‘yan giya da sauran marasa lafiya. Ina shawartar maza da kada su guji kunzugu don tsaftace dakin kwanansu,” a cewar Getumbe.
Yadda tsohuwar matata da yaranta su ka hada kai wurin yi min dukan kisa
Francis Van-Lare ya bayyana kalubalen da ya fuskanta a aurensa na baya da ya mutu. Ya bada labari dalla-dalla inda yake shawartar mutane da su kula kwarai wurin zaben aboki ko abokiyar rayuwa, LIB ta ruwaito.
Francis ya ce ya fada soyayya mai zurfi ne tun lokacin yana karatu a fannin shari’a amma mutane su ka dinga shawartarsa da ya auri macen da ta kai shekaru 40 kuma mai yara saboda sai sun fi daidaitawa.
Ya ce ya bar budurwarsa inda aka shawarceta da ta auri yaro matashi wanda za su taso tare. Bayan daukar shawarar ne ya auri mata mai yara 4.
Ana yin auren ta dinga yada hotunansu a kafafen sada zumunta wanda hakan ya ci karo da yarjejeniyarsu wacce su ka ce kada su yada komai ga jama’a.
Ya ce bayan shekaru biyu da auren, matar da yaranta su ka taru su ka lakada masa bakin duka. Ganin haka yasa yayi gaggawar sakinta.
Ya bayyana yadda itama tsohuwar budurwarsa da aka shawarar ta auri matashi bayan kammala karatu aurenta ya mutu.
Ya bayar da labarin ne don ya sanar da jama’a cewa ba daga auren mai kananun shekaru ko kuma mai shekaru dayawa bane ke sa aure yayi karko. Hasali ma fahimtar juna da jajircewa ne sinadarin aure.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com