Tsohon jarumin Kannywood, Aminu Ahalan ya bayyana a wani bidiyo da ya saki a shafinsa na TikTok inda ya dinga surutai yana zage-zage game da masu sukarsa akan yabon mawaki Rarara da hawa wakarsa da yake yi, Bakori Celebrites na Facebook ya ruwaito.
Ya fara da cewa:
“Salam, wannan bidiyon naku ne, musamman marasa kunyar nan na TikTok. Abinda nake so in gaya muku ba. Duk cikinku babu wnada ya isa, gajojin banza da na wofi.“
A cewarsa, ya kula da ‘yan bani na iya da kuma Wawayen da ke kafafen sada zumunta da su ke caccakarsa da zarar ya yabi Rarara, kuma a ya ce ba ya neman komai a wurin mawakin.
A cewarsa Rarara yana kokari kwarai wurin kyautata wa jama’a kuma shi din ba jahili bane, don lakcara ne a jami’a. Ya ja kunnen jama’a inda yace shi da babban mutum ne, kada aga yana harka a soshiyal midiya tare da jama’a amma shi din ba karamin mutum bane.
Ya yi zagi masu nauyi ga duk masa sukarsa inda yace ya wuce da saninsu, kuma su kiyaye shi tunda su jahilai ne marasa kunya da mutunci.
Ya ci gaba da cewa:
“Akan mawaki Rarara zan ci uwar kowa, banzaye, jahilai, Ass holes. Tunda ba ku da hankali, bari nima in yi alfahari. Ni lakcara ne, na fi karfinku. Kuma Rarara ya fi karfinki.
“Ban yi wa ministoci, ko sanatoci roko bane zan yi wa Rarara? Ni dai kawai ina son shi ne. Kuma ayyukan da yake yi su na burge ni. Don haka ku jahilai ne. Kuma ba ta taku nake yi ba.”
Yadda lakcara da ƴaƴansa su ka yi wa budurwa tsirara tare da lakaɗa mata baƙin duka
Wani lakcara da yaransa sun kai wa wata budurwa farmaki inda su ka yi mata tsirara tare da lakada mata dukan tsiya bayan ta samu hatsaniya da diyarsa, LIB ta ruwaito.
An dauki bidiyon Dr Fred Ekpe Ayokhai, lakcara a jami’ar tarayya ta Lafia da yaransa yayin da su ke mai wa budurwar mai suna Blessing Mathias hari a Jihar Nasarawa.
A daya daga cikin bidiyoyin, an ga Dr Fred rike da almakashi yayin da yake yankar rigar Blessing yayin da take rokonshi gafara.
Blessing ta rika rigarta da karfi da hannayenta don ta adana tsiraicinta amma yaran Dr Fred sun tilastata cire hannayenta don mahaifinsu ya yaga rigar ba tare da taba kirjinta ba.
Sannan sun nemi ta bai wa ‘yar uwarsu Emmanuella hakuri akan abinda ta yi mata a baya. Cikin biyayya Blessing ta durkusa tana ba ta hakuri, amma Emmanuella ta ki amincewa ta hakura.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com