34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Yadda wasu matasa ‘yan luwadi suka kashe kansu ta hanyar fadowa daga kan gada

LabaraiLabaran DuniyaYadda wasu matasa 'yan luwadi suka kashe kansu ta hanyar fadowa daga kan gada

Sun yaɗa hotunan su a shafin Instagram

Wasu matasa ‘yan luwaɗi su biyu sun kashe kawunan su ta hanyar faɗowa daga kan wata gada mai tsayi bayan sun sumbaci junan su. 

Matasan da aka bayyana sunan su da Tigran da kuma Arsen dai sun yaɗa wasu hotuna nasu suna sumbatar juna a shafin Instagram, tare da rubuta cewa suna murna da kawo ƙarshen rayuwar su. Kuma wannan matakin da suka ɗauka su biyun duka sun amince da shi.

Gama hakan keda wuya sai kawai matasan suka sulmiyo ƙasa daga kan gadar Davtashen mai tsawon tako 31 wacce take a Yerevan, babban birnin ƙasar Armeniya kamar yadda majiyar mu ta NY Times ta wallafa.

‘yan luwaɗin sun fuskanci tsangwama daga al’umma

Wasu kafafen cikin gida sun ruwaito cewa matasan ‘yan luwaɗin na fuskantar tsangwama ne sakamakon rashin amincewar da iyayensu suka yi da alaƙar tasu. Sunce Arsen ma ya gudo daga gidansu ne a dalilin hakan.

Wata hukumar kare haƙƙin ‘yan luwaɗi da sauran masu auren jinsi mai sun Pink Armenia ta bayyana cewa matasan nada sauran kwanaki masu yawa a rayuwar su, amma tsangwamar da suke fuskanta a wajen mutane ta sa sun kashe kawunan su.

“ ‘yan luwaɗi da sauran masu auren jinsi sun saba da zaman wariya da kuma rashin jituwa da ‘yan uwan su da sauran al’umma. Wannan abu da ya faru, ya ƙara tabbatar da cewa rayuwar mutanen mu na ‘LGBT’ a Armeniya na cikin haɗari kuma gwamnatin ƙasar bata damu da kare su ba.” inji Pink Armenia.

Mutane sun tofa albarkacin bakunan su akai

Mutane da dama sunyi mummunan tsokaci akan hotunan da waɗannan matasa suka wallafa a shafin nasu na Instagram.

Ƙasar Armeniya dai na cikin ƙasashen da ake ƙyamatar ‘yan luwaɗi da sauran masu auren jinsi a yankin turai. Ƙasar itace ta 47 cikin ƙasashe 49 da suke ɗan mutunta haƙƙin masu auren jinsi a yankin.

Aƙalla kaso saba’in (70%) na ‘yan ƙasar ta Armeniya na ganin auren jinsi a matsayin baƙon abu.

A wani labarin kuma, shahararren fasihin mawaƙin Hausa Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan waƙa ya bayyana cewa kare mutuncin Rarara ya fiye mishi takarar kujerar siyasar da ya fito.

Ala ya bayyana hakan ne a shafin shi na facebook, inda ya wallafa rubutun haɗi da hoton mawaƙi Dauda Kahutu Rarara. Ba so ɗaya ya wallafa rubutun nuna goyon bayan Rarara a shafin nashi na facebook ɗin ba.

“Yaƙin kare mutuncin Dauda ya fi yaƙin neman zaɓen ɗan takarar ɗan Majalisar tarayya agareni. Mu yi mutunci da mutuncinka, ka yi mutunci da mutuncinmu shi ne babban arziƙi na zaman tare. Takarata fansa ce a wajen kare mutunci da Hakkin DAUDA.” kamar yadda Alan ya rubuta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe