27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Kotu ta tura wani matashi gidan kaso bisa damfarar wata tsohuwa miliyoyin kudade

LabaraiKotu ta tura wani matashi gidan kaso bisa damfarar wata tsohuwa miliyoyin kudade

Wata babbar kotun jihar Kano ta yankewa wani matashi mai suna Aminu Ishaq hukuncin shekara uku a gidan kaso bisa amfani da kudin haram.

Alkali mai shari’a Nasiru Saminu shine ya zartar da wannan hukuncin a ranar 25 ga watan Oktoban 2022.

Da jikan tsohuwar aka hada baki wajen yin satar

Matashin da aka yankewa hukuncin yana daya daga cikin matasa shida da aka cafke a satar sama da Naira miliyan sha biyar (N15,000,000m) daga asusun wata tsohuwa wacce kaka ce ga daya daga cikin su (Al-Mustapha Nasir). Shafin LIB ya rahoto.

Kotun da yankewa Al-Mustapha Nasir hukunci a ranar 6 ga watan Oktoban 2022.

Matasan sun shiga hannun hukuma ne bayan an shigar da wani korafi wanda yayi zargin cewa Al-Mustapha Nasir ya sace layin wayar kakar sa, ya hada baki da abokan sa inda suka sace sama da N15m daga asusun ajiyar ta na banki ta hanyar turawa daga banki da kuma cirewa a POS.

Tuhumar da ake masa na cewa:

“Kai Aminu Ishaq, wani lokaci a shekarar 2021 a Kano, bisa ikon wannan kotun ka rike kudin da suka kai N350k, wanda kasan kudin sata ne, hakan yasa ka aikata laifin da ya cancanci hukunci a bisa sashi na 17 (a) da (b) na dokar kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta shekarar 2004.”

Ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi

Wanda ake karar ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi bayan an karanta masa.

Bisa la’akari da afuwar da matashin ya nema, Salihu Sani, lauyan dake kara ya nemi kotun da ta yanke masa hukuncin da ya dace. Lauyan dake kara wanda aka kara, Nuriyyah Musa ta nemi kotun da ta yi sassauci wurin yankewa matashin hukunci.

Alkali Saminu ya yankewa matashin hukuncin shekara uku a gidan kaso da zabin biyan tarar Naira dubu dari (N100,000).

Kotun daukaka kara tayi watsi da tuhumar da ake wa Nnamdi Kanu, shugaban ‘yan ta’addan IPOB

Wata kotun daukaka kara mai zamanta a birnin tarayya Abuja ta wanke shugaban haramtacciyar kungiyar ‘yan ta’adda, Indigenous People Of Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu.

Gwamnatin tarayya na tuhumar Nnamdi Kanu a babban kotun tarayya dake Abuja, bisa laifuka 15 da suka hada da tawaye da ta’addanci, laifukan da ake zargin ya aikata a lokacin da yake gangamin jagorantar ‘yan aware

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe