34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Budurwa ta cinnawa kwalin digirin ta wuta a bainar jama’a, bidiyon ya dauki hankula

LabaraiBudurwa ta cinnawa kwalin digirin ta wuta a bainar jama'a, bidiyon ya dauki hankula

Wata budurwa mai suna Bridget Thapwile Soko, ‘yar kasar Malawi ta cinnawa kwalin digirin ta wuta.

Budurwar wacce ta karanci ilmin kasuwanci ta cinnawa kwalin digirin na ta wuta ne a gaban jama’a.

Dalilin da ya sa budurwar ta kona kwalin digirin

Bridget Thawile Soko ta fusata ne bayan ta kwashe shekara hudu tana zaman kashe wanda ba tare da ta samu aikin yi ba tun da ta kammala jami’ar Exploits a kasar Malawai. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

A wani bidiyon da aka dauka kai tsaye a TikTok, matashiyar budurwar ta rera waka da shagube ga duk wanda ya ki samar mata da aikin yi ko gayyatar ta zuwa neman aikin yi.

Ta bayyana cewa ya fiye mata ta kona kwalin digirinta ta bar na auren ta. Sautin muryoyin da aka jiyo ya nuna cewa akwai mutane a kusa da ita wadanda suke cikin kaduwa lokacin da take kona kwalin.

Hukumar jami’ar ta fitar da martani kan lamarin

A halin da ake ciki, jami’ar da ta yi karatu ta fitar da martani bayan aika-aikar da Bridget tayi ta yadu a duniya.

A cewar shugaban jami’ar Exploit, Desmond Bikoko, budurwar tayi hakan ne kawai domin ta zubar da kimar makarantar.

A wata takarda da hukumar makarantar ta fitar a ranar 21 ga watan Oktoban 2022, sun yi Allah wadai da abinda ta aikata sannan kuma sun soke kwalin digirin da ta samu a jami’ar.

Takardar na cewa:

“Cikin takaici mun samu labarin cewa kin dauki faifan bidiyo kina kona kwalin digirin da muka baki bayan kammala karatun ki a jami’ar Exploit sannan kika watsa a kafafen sada zumunta.”

“Mun fahimci kin yi hakan ne domin ki ci mutunci da zubar da kimar jami’ar. Don haka jami’ar ta soke kwalin digirin da aka baki a fannin ilmin kasuwanci. Za mu sanya wannan hukuncin na mu a kafafen watsa labarai.”

“Don haka, daga yanzu ke ba dalibar da ta kammala karatu ba ce a jami’ar Exploit, sannan kwalin digirin ki ya tashi daga aiki nan take.”

Na nemi aiki har guda dubu biyar 5000 bayan kammala digiri na na 2 amma na bige da sayar da dafaffen kwai a kan titi – Inji wani magidanci 

Wani matashi mai suna Denis Obili Ogola, ya bada labarin cewa yana da digiri har guda biyu, amma ya kasa samun wani cikakken aiki daya kwakkwara, bayan kammala digiri na biyu a jami’ar da yayi. 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe