Shahararren fasihin mawaƙin Hausa Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan waƙa ya bayyana cewa kare mutuncin Rarara ya fiye mishi takarar kujerar siyasar da ya fito.
Takara ta fansa ce ga mutuncin rarara
Ala ya bayyana hakan ne a shafin shi na Facebook, inda ya wallafa rubutun haɗi da hoton mawaƙi Dauda Kahutu Rarara. Ba so ɗaya ya wallafa rubutun nuna goyon bayan Rarara a shafin nashi na facebook ɗin ba.
“Yaƙin kare mutuncin Dauda ya fi yaƙin neman zaɓen ɗan takarar ɗan Majalisar tarayya agareni. Mu yi mutunci da mutuncinka, ka yi mutunci da mutuncinmu shi ne babban arziƙi na zaman tare. Takarata fansa ce a wajen kare mutunci da Hakkin DAUDA.” kamar yadda Alan ya rubuta.
Kada ka bari su rinjaye ka
mutane da dama dai sunyi tsokaci akan rubutun da mawaƙin ya wallafa a shafin nasa. Wasu suna ganin cewa bai dace yace wani abu ba dangane da rikicin da yake faruwa tsakanin Rarara da waɗanda yake rikicin da su.
“Hmm! Mu dole mufadama gaskiya ALA mutuncinka ba daya yake Dana Rarara ba , takun ku ba iridaya bane acikin Al’ummar qasaba Kai Dan gwagwarmaya ne nagaske Wanda kake tausayi Al’ummar ka duba da zubin wakokinka haka Abun yake har zuciyarka, kada kabari irinsu Rarara yan kasuwar saida basira su rinjayeka.” inji wani Jamilu Ya’u Alrafidiy
Shi kuma wani mai Suna Musa Isa Turaki roƙon Ala yayi akan ya cire hannun sa a cikin batun domin a cewar shi tsarin waƙoƙin Ala dana Rarara ba iri ɗaya bane.
“Kanada mutunci da kima a idon kowa domin baka cin mutuncin mutane a wakokinka. Rarara sabanin haka ne daga cin mutuncin mutane se zagi da gori. Don Allah ka cire hannunka daga kare Rarara ka barshi ya girbi abunda ya shuka.” inji Musa Isa Turaki.
Mutane basu san yadda abun yake ba
Kafin wannan iƙirarin, mawaƙi Ala yayi wani rubutun cikin shaguɓe inda a ciki yake nuna cewa wasu da yawa basu san yadda faɗan yake ba. Da sun sani to lallai da basu ce komai ba.
“Kallo ya koma sama ga dukkan Alamu. Mugun madambaci shagon guramaɗa. Da yawa daga masu faɗa dakai basu san abokin faɗan ba. Da sun sani da basu yadda sun gwada wa kucciya baka ba.” inji Aminu Alan waƙa.
Da dama daga cikin masu tsokaci akan rubutun da Alan yayi sun nuna cewa bai kamata ace ya tsoma baki a cikin rikicin ba. Sai dai kuma wasu na ganin hakan da ala yayi nuna hallaci ne ga Rarara.
A wani labarin na daban kuma, kunji iyayen wata mata sun gano cewa mijin nata ya ɓoye musu batun mutuwar ta har na tsawon wata tara, inda da suka gano sai ya bayyana musu cewa ya manta ne shi yasa bai sanar dasu ba.
Wani mutum mai suna Abubakar ya wallafa a shafin shi na tuwita mai suna Fadhlu_S labarin yadda wani miji ya binne matar shi da ta mutu wata tara da suka gabata ba tare da sanar da iyayen ta ba.
Kamar yadda Fadhlu ya bayyana, iyayen matar basu sani ba har sai Asabar ɗin nan, 22 ga Oktoba 2022, bayan da wata mata taga ƙabarin nata, inda daga nan ne ta tuntuɓe su don sanar dasu.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com