‘Yan uwan wani mutum su na ta zundensa bayan ya fada tarkon soyayyar wata mata mai cutar makanta kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Mutumin wanda asali daga Arusha yake, cikin kasar Tanzania, yana tsaka da neman halaliyarsa sai ya hadu da wata makauniya wacce yaji kaf duniya babu wacce tayi masa sai ita.
Mutumin mai suna Rashidi Apahamanyi Musasigye ya bayyana kudirinsa na auren Lilian.
Wannan lamarin ya bai wa Lilian mamaki inda taga mutumin da ba ya da wata nakasa ya bukaci ya zabe ta a matsayin matarsa, kamar yadda Afrimax English ta bayyana.
Anan ne Lilian ta bayyana wa Rashidi labarin yadda mijinta ya bar ta bayan sun haifi yara biyu ba tare da sake waiwayarta ba. Hakan bai da Rashidi ya sauya niyyarsa ba, anan ne yace mata yana son rayuwa da ita har karshen rayuwarsa.
‘Yan uwansa sun nuna masa cewa bai dace ya aureta ba, zai fi kyau idan har ya auri wacce za ta iya tallafa masa maimakon mai nakasa.
Duk da haka, sun yanke shawarar yin aurensu inda su ka ci gaba da rayuwa cikin soyayya da kauna. Sai dai bayan shekaru kadan aka kusa halaka Rashidi ba tare da ya yi komai ba, wanda daga bisani kuma aka tura shi kurkuku.
Bayan wani lokaci kadan ya makance. Rashidi ya zargi ‘yan uwansa da yi masa mugun aikin, inda yace ba su da niyyar ganin ya ci gaba.
Yar uwata ce ta yi mini asiri na makance saboda mai kudi ya yi alkawarin zai aure ni – Makauniya
Wata mata ‘yar kasar Ghana mai fama da larurar makanta, da aka bayyana sunanta da Portia Ama, ta bayyana labarinta marar dadin ji kan yadda aka yi mata asiri da ya sanya ta tsinci kanta cikin wannan hali na makanta.
Matar wacce ke zaune a wani kauye a yankin Central Region, ta zargi cewa ‘yar uwarta ce ta yi mata asiri saboda tana kishi akan wani mai kudi da ya yi mata alkawarin zai aureta a lokacin da tana ‘yar shekara 13 a duniya.
A wata hira da Ama ta yi da D.J Nyame na gidan talabijin din SVTV, ta yi zargin cewa ‘yar uwartan wacce a da take bautawa gumaka, ta sha alwashiin ganin ba ta samu nasarar auren wannan mutumi mai arziki ba, hakan ya sanya ta mai da hankali wajen ganin ta lalata mata rayuwa, inda ta shiga yi mata asiri har sai da ta ga ta makanta ta.
A cewarta ta ziyarci Fastoci da dama don ganin idonta ya dawo amma duka kokarin da take a banza.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com