Wani matashi ya bayyana halin da yake ciki yanzu haka bayan budurwarsa wacce su ka yi shekaru uku tare ta dawo dakinsa inda ya koma kwana akan kujera, Legit.ng ta ruwaito.
Matashin ya ce bai gano cewa budurwarsa warin rubabben kwai take yi ba sai da ya dawo da ita dakinsa inda ya gane cewa tana daukar kwanaki kafin tayi wanka.
Ya ce saboda ba ta wanka yasa ya dena kwana a gefenta saboda tsakar dare warin jikinta ke addabarsa ya kasa bacci.
A cewarsa, ashe sau daya take wanka a sati biyu, kuma komawarta dakinsa ne yasa ya gano wannan boyayyen sirrin dangane da ita kamar yadda The Sun ta ruwaito.
Ya kara da cewa bai taba tunanin cewa budurwar da ya bai wa kyautar zuciyarsa kazama bace sai yanzu. A cewarsa dakyar ake samu tayi wanka a mako guda.
Ya ce dama ya kula da cewa tana da warin jiki sai dai bai damu ba don yasan mutum tara yake bai cika goma ba, sai dai bayan dawowarta dakinsa ne ya gano silar hakan. Ya ci gaba da cewa:
“Bayan watanni kadan da dawowarta har na gundura, kasancewar warin da take yi ya tsananta. Na dade ina zaunar da ita don mu tattauna amma abin ya ci tura.”
Ya ce har hassala tayi a lokacin da ya zaunar da ita don gaya mata cewa gaskiya tana wari, amma sai ta fashe da kuka tana cewa babu abinda ya dame shi.
Yanzu haka dai ya gaji ne, shiyasa ya bukaci shawarar jama’a don su samar masa mafita akan yadda zai bullo wa lamarin.
Halaye masu kyau da na koya a wajen Musulmai -Wata budurwa Kirista
Wata budurwa mabiyar addinin kirista ta bayyana wasu muhimman dabi’u da ta koya daga wajen Musulmai.
A cikin wani bidiyo da budurwar mai suna Gayobi Achawa ta saka a shafin TikTok, ta bayyana cewa ita ba Musulma bace amma tana da ‘yan’uwa Musulmai a cikin danginta.
Halayen da ta koya daga wajen musulmai
Budurwar ta bayyana cewa wadannan halayen na Musulmai da ta koya wadanda suke matukar birgeta, ta koye su ne a wajen ‘yan’uwanta da kuma wajen yin aiki tare da Musulmai.
Ga jerin su kamar haka:
1. Mata Musulmai sun nuna mana cewa ba sai mace tayi shigar banza ba kafin kyawunta ya bayyana. Mata Musulmai za su rufe jikin su amma za ka ga kyawun su yayi matukar bayyana.
2. Biyayya, Musulmai nada matukar biyayya kan addinin su. Ba musulmin da zai bari a taba darajar Al-Qur’ani, manzon Allah (SAW) da Allah (SWT). Idan abota ta hadaku, to lallai komai rintsi komai wuya za su kasance tare da kai.
3. Musulmai ba munafukai bane, Musulmai ba ruwan su da munafurci idan suka ce za suyi abu to lallai gaskiyar kenan za suyi shi.
4. Yadda mata suke tsarkake jikin su bayan sun yi amfani da bandaki.
5. Kalmomi guda masu matukar muhimmanci wadanda suke min dadi a baki sune Insha Allah, Masha Allah da Alhamdulillah.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com