24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Zaben 2023: Tinubu ya gwangwaje jaruman Kannywood da N50m don su bunƙasa masana’antar

LabaraiKannywoodZaben 2023: Tinubu ya gwangwaje jaruman Kannywood da N50m don su bunƙasa masana'antar

Yayin da zaben shugaban kasa na shekarar 2023 ke karatowa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC ya bai wa jaruman Kannywood gudunmawar 50 don ci gaban masana’antar, Fim Magazine ta ruwaito.

Ya bayar da kyautar ne gare su yayin da ya je taron da jaruman masana’antar su ka shirya masa wanda aka yi ranar Lahadi a fadar gwamnatin Jihar Kano.

Dama da farko Abdul Amart Maikwashewa ya yi jawabi inda yace an shirya taron ne don matasa ‘yan fim masu goyon bayan tafiyar Tinubu na karkashin gidauniyar Kannywood domin kara tasirinsa a cikin ‘yan fim din.

Hakan yasa su ka taru don su nuna masa yadda su ke bayansa don tabbatar da ganin ya samu nasara.

A bangaren nasa jawabin, Dr Ahmad Sarari, shugaban kungiyar masu shirya finafinai ta Najeriya, MOPPAN na kasa, ya bayyana Kannywood da kuma wata babbar masana’anta da ke kawo kudaden shiga da samar da sana’a ga matasa, hakan yasa yayi kira ga Tinubu da ya duba yadda masana’antar take idan har aka kai ga nasara.

A bangarensa, Alhaji Sani Mu’azu, shugaban MOPPAN ya nemi Tinubu ya sanya ‘yan fim a cikin yakin neman zabensa saboda yadda jama’a ke karbarsu tare da masoyansu masu yawa a fadin kasar.

Gwamna Samuel Lalong, shugaban kwamitin yakin neman zaben Tinubu, ya tabbatar da cewa za su sanya su a tafiya, sannan ya ba su kyautar Naira miliyan 50 ga Kannywood don inganta masana’antar.

Kungiyoyin da ke karkashin masana’antar dukkansu sun samu nasarar halartar taron.

Ga masu bata sunan ‘yan Kannywood: Duk wanda yace kule, za mu ce cas!, Tijjani Faraga

Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Malam Tijjani Faraga ya ce akwai masu ilimi da dama a cikin masana’antarsu don haka ba za su sake yarda wani ya bata sunansu ba.

Ya bayyana hakan ne ta wani rubutu da yayi ya tura wa Mujallar Fim inda yace:

Mu na da isassun masu ilimi a Kannywood wadanda a duk lokacin da masu neman bata sunanmu su ka zaburo su ka ce kule, za mu ce musu cas.

Don haka duk wanda daga yanzu ya ke neman cin zarafinmu, to sai dai kotu ta raba mu don mu ma ‘yan kasa ne. Ba mu da wata sana’ar da ta wuce fim.”

A cewarsa, yadda ake karatu a fannin likitanci ko lauya, injiniya da sauransu, duk haka su ma su ka yi karatu a kan shirin fim.

Ya ce bai da dalilin da zai yarda wanda bai taba shiga cikinsu ba ya zagaya yana bata sunan sana’arsu a idon duniya. Faraga ya ci gaba da cewa:

Ai kun ji labarin yadda Alhaji Hamisu Lamido Iyantama ya kai wani kotu bayan ya yi maganganu barkatai akan ‘yan Kannywood. Kishin abin ne ya sanya nayi wannan rubutun don in sanar da cewa mu na da masu ilimi wadanda idan aka yi mana wani abu za mu dauki mataki akai.

Abinda Iyantama yayi abu ne ake cewa ‘eye opener’. Dama mun yi shiru ne mu na kallon mutane ana jin abubuwan da su ke fada. Kuma a harkarmu mun shirya ne don ta zama sana’armu kuma gatanmu.

Toh duk wanda yayi yunkurin kawo mana cikasa, ba za mu bar shi ba.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe