Jiragen yakin sojojin sama na Najeriya (NAF) sun yi luguden wuta a sansanin wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Halilu Sububu, a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Halilu Sububu ana tunanin cewa shine shugaban ‘yan bindiga wanda yafi kowa tarin dukiya a jihar.
Harin jiragen yakin yayi sanadiyyar halaka ‘yan bindiga da dama inda akalla ‘yan bindiga 30 suka sheka barzahu. Jaridar Premium Times ta rahoto.
Babu tabbacin ko an halaka shugaban ‘yan bindigan
Sai dai, ba a da tabbacin cewa ko Halilu Sububu ya halaka a yayin harin.
Halilu Sububu wanda ya fito daga garin Sububu a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, shine babban mai safarar makamai wanda yayi kaurin suna wurin samar da makamai ga sauran ‘yan ta’adda a jihohin Zamfara da Katsina.
Halaka mayakan Sububu ya biyo bayan samun wani bayanin sirri wanda ya bayyana cewa ya shirya wani taron safe da wasu daga cikin dakarun sa, a sansanin sa dake karamar hukumar Maradun ta jihar.
Yadda aka shirya kai harin
Wani babban jami’in soji ya bayyana cewa bayanin sirrin da aka samo ya nuna ainihin inda sansanin Sububu yake, inda yake ajiye makamai, babura da sauran wasu kayayyakin sata.
“Bayan kwashe kwanaki ana shawagi kan wuraren biyu domin tabbatar da ingancin bayanin sirrin, jiragen yakin NAF, da safiyar ranar 21 ga watan Oktoban 2022 sun yi luguden wuta a wajen taron da kuma sansanin.”
“Kimanta barnar da harin tayi ya nuna cewa an lalata wurin taron da sansanin. Bayanan da aka samu daga wajen mutanen yankin ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga da dama sun halaka a dalilin harin a wurin taron, sai dai babu tabbacin cewa ko an halaka Halilu Sububu a harin.” A cewar jami’in.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com