24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Wani matashi ya fara tattaki daga Gombe zuwa Abuja domin Tinubu

LabaraiWani matashi ya fara tattaki daga Gombe zuwa Abuja domin Tinubu

Wani matashi mai shekara 31 a duniya, Mohammed Umar, a ranar Litinin ya fara tattaki na tsawon kilomita 425 daga Gombe zuwa birnin tarayya Abuja, domin neman magoya baya ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Umar, wanda mamba ne a kungiyar magoya bayan Tinubu mai suna TinKas Tinubu/Shettima Support Group, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) jim kadan fara tattakin sa a Gombe cewa yayi wannan yunkurin ne domin nuna goyon bayan sa ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a yayin da ake tunkarar babban zaben 2023 dake tafe. Jaridar Daily trust ta rahoto.

Ya bayyana cewa kungiyar su ta nemo magoya baya a yankin Arewa maso Gabas ga jam’iyyar APC domin tabbatar da cewa ta samu nasara a kowane mataki a zaben 2023.

Ya bayyana dalilan sa na yin tattakin

“Tinubu ya zabi namu, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar sa; abinda yakamata mu yi masa shine mu nemo masa magoya baya wadanda za su bashi kuri’u masu yawa daga yankin Arewa maso Gabas.

“Tinubu ya nuna kwarewa da cancanta, haka ma Kashin Shettima. Goyon bayan takarar su domin samun nasarar su a zaben 2023 zai amfani ‘yan Najeriya.”

“Ni da kai na zanje Abuja domin gayyato shugabannin mu Sanata Tinubu da Shettima su zo su kaddamar da ofishin yakin neman zaben mu a jihar Gombe.” Inji shi.

Yayi kyakkyawan shiri da tanadi

Matashin wanda yake da yara uku a duniya ya bayyana cewa a shiryawa tattakin sosai yadda yakamata.

“Na dauka maganin zazzabin cizon sauro watakila ko zan fada rashin lafiyar a yayin tattaki na zuwa Abuja. Tattakin zai kasance da rana ne kawai, idan dare yayi zan nemi wurin jami’an tsaro na gabatar musu da kai na domin na kwana a wajen su.

“Iyalai na sun goyi baya na akan wannan yunkurin nawa. Na samu cikakken goyon baya da fatan nasara daga wajen iyalai na.” A cewar sa.

Nayi alƙawarin dorawa daga inda Buhari ya tsaya kan matsalar tsaro – Tinubu

Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata yayi alƙawarin ɗorawa daga inda gwamantin Buhari ta tsaya kan matsalar tsaro, tattalin arziki da sauransu in aka zaɓe shi a 2023.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake zayyano muhimman abubuwa guda uku da zaiyi in aka zaɓe shi a zaɓen 2023 mai zuwa. Ya shaidawa Buhari cewa zai tafiyar da ayyukan da ya ƙaddamar bayan ya gama a 2023 

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe