24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Yadda na ke basaja ina samo bayanai ga ‘yan bindiga ga -Wani almajiri

LabaraiYadda na ke basaja ina samo bayanai ga 'yan bindiga ga -Wani almajiri

Wani karamin yaro wanda almajiri ne ya bayyana yadda yake samo bayanai ga ‘yan bindiga.

Almajirin mai suna Zaharaddeen Tasi’u mai shekara goma a duniya ya bayyana cewa ya fito ne daga garin Bakwai cikin jamhuriyar Nijar.

Yadda yake batar da sawu yana samo bayanai ga ‘yan bindiga

Almajirin a cikin wani bidiyo da shafin Nishadi TV ya saka a Facebook, ya bayyana cewa ‘yan bindiga na turo su zuwa cikin gari domin yi musu leken asiri.

A cewar sa su kan shigo cikin gari da rana domin duba mutanen da suke da dukiya da wadanda suke da shanaye domin kai rahoton ga ‘yan bindiga a cikin daji.

Bayan sun mika rahoton leken asirin da suka yi ga ‘yan bindiga, can cikin dare sai su taho tare da ‘yan bindigan domin sace mutanen da ke da dukiya, da kuma kora shanayen zuwa cikin daji.

Almajirin ya iya amfani da bindiga

Almajirin ya bayyana cewa bai wani dade yana aiki tare da ‘yan bindigan ba, amma a dan lokacin da yayi da su har ya fara isa sarrafa bindiga.

Ya bayyana cewa da zuwan sa wurin ‘yan bindigar aka fara koya masa yadda zai yi amfani da bindiga.

Ga bidiyon a nan

Matsalar tsaro na kara tabarbarewa a kasar nan duk kuwa da kokarin da jami’an tsaro ke yi wajen ganin sun dakile matsalar tsaron.

Jami’an DSS sun cafke wani soja mai safarar makamai ga ƴan ta’adda a Abuja

A wani labarin na daban kuma, jami’an DSS sun samu nasarar cafke wani soja mai safarar makamai ga ‘yan bindiga.

Jami’an hukumar farin kaya ta DSS sun cafke wani soja a Abuja bisa zargin bada haya da siyar da bindigu ga masu garkuwa da mutane.

Sojan yana aiki a sansanin Muhammadu Buhari a Tungan-Maje a birnin tarayya Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an cafke sojan ne satin daya gabata a kusa da wurin shaƙatawa na Dankogi a Zuba tare da haɗin guiwar mambobin ƴan sakai na yankin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe