35.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Yadda saurayina ya lakaɗa min dukan tsiya bayan kwashe shekaru mu na zaman dadiro, Muneerat

LabaraiYadda saurayina ya lakaɗa min dukan tsiya bayan kwashe shekaru mu na zaman dadiro, Muneerat

A wani bidiyo wanda Muneerat Abdussalam, fitacciyar mai sayar da magungunan mata da maza a kafafen sada zumuntar zamani ta saki cike da hawaye ta yi karin bayani.

Dama tun safiyar Litinin ta bayyana yadda bariki tayi mata atishawar tsaki inda yanzu haka ta rasa makama kasancewar ko kudin magani ta rasa.

A bidiyon wanda aka ga yadda saurayinta ya molar mata da fuska saboda tsabar dukan da yayi mata, ta bayyana yadda ta kai kara caji ofis amma ‘yan sanda su ka mayar da maganarta shirme.

Ta ce ta kwashe lokaci mai tsawo su na zama da matashin wanda yayi alkawarin aurenta, ashe dan daba ne kuma cikakken dan ta’adda ne bata sani ba.

Ta shaida yadda yake zuwa dakinta da tsakar dare tare da balle mata kofa sannan ya tumurmusata da zarar ta yi masa kankanin abu wanda ya hassala shi.

Ta ce ya tsere mata da kayan da ta aike shi ya sanya mata a mota masu kimar dubu dari uku da ‘yan kai. Ta ci gaba da shaida cewa har guduwa tayi daga garin da suke don ta tsira daga sharrinsa bayan samun labarin ta’addancinsa.

A cewarta tana neman taimakon jama’a kuma ta yi nadamar gabadaya abubuwan da ta aikata a rayuwarta na bariki da biye-biyen maza.

Ta bayyana yadda take rayuwa cike da tashin hankali sannan saurayin nata yana ba ta hakuri idan sun yi fada daga bisani kuma yayi mata abinda ya zarce na baya.

Bayan zaman dadiron shekaru 11 da haihuwar yara 2, mawakiya Shakira da saurayinta sun rabu

Mawakiyar kasar Kolombiya, mai shekaru 45, Shakira da saurayinta, Gerard Piqué, mai shekaru 35 sun rabu bayan shekaru 11 da su ke tarraya tare da haihuwar yara biyu, Daily Mail ta ruwaito.

A shekarar 2017 aka dinga yada labarin rabuwar masoyan inda aka ce sun dena zama tare. Inda Shakira ta bayyana rashin jituwar da ke tsakaninsu a wata waka da ta saki.

Kamar yadda ta saki wasu baituka:

“Wurin kokarin cikasa ka, ta farfashe; na ja kunnenka amma ba ka ji ba; sai daga baya na fahimci karya ka ke yi….”

Tun shekarar 2011 masoyan su ke tare, sun hadu ne yayin da ta ke shirya bidiyon wata wakar da ta fi ta gasar kofin kwallon duniya mai suna Waka Waka.

Ta bayyana batun rabuwarsu

Mawakiyar mai shekaru 45 ta tabbatar da rabuwarsu yayin da ake tsaka da yada labarai akan cewa ya ha’inceta da wata.

Jaridar Spain ta El Pariodico ta ruwaito cewa sun raba gari ne bayan makwanni kadan da mawakiyar ta fatattaki Pique.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe