Fitacciyar mai maganin mata, Muneerat Abdulsalam ta bayyana halin da take ciki na kunci da takaici kasancewar bariki ta yi mata atishawar tsaki. A wata wallafa da tayi yau, an ga yadda idonta ya kumbura har yace tana neman makancewa sakamakon mawuyacin yanayin da ta shiga.
A cewarta ba ta da ko kudin da za ta siya wa kanta Paracetamol saboda tsananin talaucin da ke damunta kuma ta tabbatar da shashanci da karuwancin da tayi.
Ta ce wannan kadai ya ishi jama’a izina musamman kananun yara masu tasowa su gane cewa bariki ba abin yi bane. Ga dai wallafar da tayi a shafinta:
“Oh ni Muneerat Abdulsalam haka ratuwata ta koma? Ko kudin sayan paracetamol banidashi kuma ba mai bani, na zama abin kwatance a idon duniya, gani ga wane ya ishi wanne soron Allah.
“Nayi nadaman duka karuwancinda nayi diga baya, da duka shashanci, da barikanci, wannan ai shi ake cewa hisabi tun baka mutu ba, toh karku kuskura ku sawa yaranku suna munira, kuma inaso ku maidani abin kwatance ga yaranku da jikokai, ina cikin nadamar rayuwar danayi diga baya, Allah ka yafemin.”
Allah dai ya kyauta ya kuma shirya mana zuri’a.
Yadda Muneerat Abdulsalam mai kayan mata ta sha zagi bayan ta nemi a hada mata kudi don tallafa wa talakawa da Ramadan
Fitacciyar mai sayar da magungunan mata, Muneerat Abdulsalam ta sha caccaka da zagi a kafar sada zumuntar Facebook bayan ta nemi tallafi daga mutane don ta taimaka wa talakawa.
A wata wallafar da ta yi a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ta sanya lambar asusun bankinta tana neman taimako don tallafa wa masu kananun karfi amma bata samu komai ba sai N1,500.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com