Wata budurwa mabiyar addinin kirista ta bayyana wasu muhimman dabi’u da ta koya daga wajen Musulmai.
A cikin wani bidiyo da budurwar mai suna Gayobi Achawa ta saka a shafin TikTok, ta bayyana cewa ita ba Musulma bace amma tana da ‘yan’uwa Musulmai a cikin danginta.
Halayen da ta koya daga wajen musulmai
Budurwar ta bayyana cewa wadannan halayen na Musulmai da ta koya wadanda suke matukar birgeta, ta koye su ne a wajen ‘yan’uwanta da kuma wajen yin aiki tare da Musulmai.
Ga jerin su kamar haka:
1. Mata Musulmai sun nuna mana cewa ba sai mace tayi shigar banza ba kafin kyawunta ya bayyana. Mata Musulmai za su rufe jikin su amma za ka ga kyawun su yayi matukar bayyana.
2. Biyayya, Musulmai nada matukar biyayya kan addinin su. Ba musulmin da zai bari a taba darajar Al-Qur’ani, manzon Allah (SAW) da Allah (SWT). Idan abota ta hadaku, to lallai komai rintsi komai wuya za su kasance tare da kai.
3. Musulmai ba munafukai bane, Musulmai ba ruwan su da munafurci idan suka ce za suyi abu to lallai gaskiyar kenan za suyi shi.
4. Yadda mata suke tsarkake jikin su bayan sun yi amfani da bandaki.
5. Kalmomi guda masu matukar muhimmanci wadanda suke min dadi a baki sune Insha Allah, Masha Allah da Alhamdulillah.
Wata baturiya ta musulunta bayan karanta Al-Qur’ani
A Wani labarin na daban kuma, wata Baturiya ta shiga musulunci bayan ta karanta Al-Qur’ani mai girma.
Bayan ta karanta Al-Qur’ani mai girma sau huɗu a wata ɗaya, wata mata mai suna Maryum a birnin Plymouth wacce ta taso cikin addinin kirista ta musulunta.
Wannan matakin da ta ɗauka na musulunta ya ƙada hantar ƴan’uwanta da abokai, inda har kakar ta ke bayyana musuluntar ta a matsayin ta wani ɗan lokaci ce.
Maryum ta taso a gidan mabiya addinin kirista sannan tayi imani da Allah. Bayan ta fara girma ta wuce shekara goma a duniya, sai ta fara ja da baya, ta kasa fahimtar alfanun zuwan coci ranar Lahadi, amma dai ta cigaba da tafiya a hakan saboda abinda aka koya mata kenan.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com