34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Wata 9 mijin bai fada ma iyayen matar shi cewa ta mutu ba

LabaraiWata 9 mijin bai fada ma iyayen matar shi cewa ta mutu ba

Mijin ya ce ya manta bai sanar dasu ba

Wasu iyayen wata mata sun gano cewa mijin nata ya ɓoye musu batun mutuwar ta har na tsawon wata tara, inda da suka gano sai ya bayyana musu cewa ya manta ne shi yasa bai sanar dasu ba.

Wani mutum mai suna Abubakar ya wallafa a shafin shi na tuwita mai suna Fadhlu_S labarin yadda wani miji ya binne matar shi da ta mutu wata tara da suka gabata ba tare da sanar da iyayen ta ba.

Wata mata ce ta sanar dasu

Kamar yadda Fadhlu ya bayyana, iyayen matar basu sani ba har sai Asabar ɗin nan, 22 ga Oktoba 2022, bayan da wata mata taga ƙabarin nata, inda daga nan ne ta tuntuɓe su don sanar dasu.

Jin hakan keda wuya sai iyayen matar suka kira mijin sannan suka tambaye shi ko menene gaskiyar zancen. Kada bakin shi keda wuya sai ya ce musu shi ya manta ne bai sanar dasu cewa ta mutu ba.

Sai dai kuma Fadhlu ya caccaki mijin, inda ya kira shi da azzalumi sabili da ya bar wayar matar a kunne, kira nata shigowa ba tare da ya na ɗaga wa ba, har zuwa sanda wata taga ƙabarin sannan ta sanar da iyayen matar.

Ya bar wayar matar a kunne ana ta kira

“Eh ya mance, amma kuma sai ya bar wayar tata a buɗe ana ta kira ba tare da ana amsawa ba. Sai da wata mata taga ƙabarin jiya a maƙabarta sannan sai ta kira iyayen ta, wanda a sannan ne suka sani. Sun tuntuɓi mijin inda anan ne yake bayyana musu cewa eh lallai ta mutu wata tara da suka gabata, amma ya mance bai sanar dasu ba.

“Wasu mutanen azzalumai ne wallahi, matar ka ta mutu watanni 9 da suka wuce, amma kuma ka mance ka kira iyayen ta. Ka cigaba da yima wayarta caji amma ka ƙi amsa kiraye-kirayen da ake mata. Ina! Akwai hisabi.” Fadhlu ya rubuta.

A wani labarin, kunji wani miji ya rushe gidan da ya ginama iyayen matar shi da kuma wanda ya gina mata sakamakon rabuwa da tayi da shi ta koma ta auri wani mutumin daban.

A ɗan gajeren bidiyon da ya karaɗe kafafen sadarwar zamani, an ga mutumin mai suna Francis Banda ɗan ƙasar Malawi tare da wasu mutane suna ta rushe gidan da ya gina ma matar shi da kuma wanda ya gina ma iyayenta biyo bayan rabuwa da tayi dashi taje ta auri wani mutumin.

Malawi 24 ta ruwaito mutumin ya na bayyana cewa shekarun su goma sha uku tare da matar a zaman aure. Ya kuma bayyana cewa ‘ya ‘ya uku suka haifa a wannan lokaci na auren nasu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe